Gagaruman Abubuwa 3 da Za Su Faru a 2024, Malamin Addini Ya Yi Hasashe
- Saura yan kwanaki a shiga sabuwar shekara kuma ya kan zo da abubuwa da kalubale da dama
- A baya-bayan nan ne wani malamin addini, Prophet Abel Boma, ya yi hasashen abubuwan da za su faru gabannin sabuwar shekara
- Daga cikinsu, Prophet Boma ya bukaci yan Najeriya da duniya baki daya su shirya ma wasu matsaloli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Port Harcourt, jihar Rivers - Prophet Abel Tamunominabo Boma ya ce akwai makirci da dama a shekarar 2024.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a dandalinsa na YouTube, Prophet Boma ya ce harda Kiristoci cikin masu kulla makircin.
2024: "Makarkashiya za ta yi yawa", Boma
Malamin addinin ya gargadi mutane a kan su yi taka-tsan-tsan a huldarsu da sauran mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake ci gaba da jawbai, Prophet Boma ya yi karin wasu hasashe biyu.
Ya ce:
"Makarkashiya za ta yi yawa a 2024. Kiristoci, wadanda ake ganin shiryayyu, sune za su zama makirai na lamba daya. Kiristoci ne za su lashe kaso 80 cikin dari.
"Na ga manyan bayin Allah, sun zauna sannan sun kulla makarkashiya a kan wani.
"Wasu daga cikin fastocinku za su ajiye littafi mai tsarki a 2024. Za ki ga yar'uwarki ta kut da kut ta hada maki makirci a 2024.
"Allah ya fada mani kuma na ji da kyau; ina matukar tsoro."
Ya ci gaba da cewa:
"Rashin lafiya mai kama da korona zai zo a 2024. Allah ya ce na fada maku cewa idan za ku yi tafiya, ku yi tafiya da katin shaidar karbar rigakafinku na 2023.
"Haka kuma, za a samu karancin maza.
"Sannan, Shugaban kasa Bola Tinubu, ku yi masa addu'a. Ina kira gareku da ku yi masa addu'a, saboda idan ya mutu, za mu koma gidan jiya. Na san ba za ku so ganin mutum kamar Kashim Shettima, dan arewa a matsayin shugaban kasa ba."
Kalli bidiyon hasashen nasa a kasa:
Primate Ayodele ya yi hasashe kan 2024
A wani labarin kuma, mun ji cewa Primate Elijah Ayodele ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta inganta yanayin tattalin arziki a kasar.
Ayodele ya yi hasashen cewa idan har aka gaza yin haka, za a yi gagarumar zanga-zanga kan gwamnatin APC a 2023.
Asali: Legit.ng