Farin Ciki a Najeriya Yayin da Matatar Man Dangote Ta Fara Aiki, Ta Fara da Ganga Miliyan Daya
- A wani sabon ci gaba da Najeriya ta samu, matatar man Dangote ta fara aiki, inda ta soma da karbar danyen mai ganga miliyan daya
- Aliko Dangote, shugaban rukinin kamfanonin Dangote ya bayyana cewa matatar za ta rinka tace kalla ganga dubu 350 a kowacce rana (bpd)
- Matatar ta kuma bayyana cewa nan da makonni uku masu zuwa za ta karbi karashen danyen man da za ta tace daga kamfanin NNPC da ExxonMobil
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Legas - Matatar mai ta Dangote ya sanar ds fara karbar ganga miliyan daya ta danyen dan Agbami daga kamfanin hada-hadar mai ta duniya mai suna Shell (STASCO).
A cewar wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Juma'a, jirgin ruwa na STASCO ya isa tashar sauke kaya ta matatar (SPM), inda aka juye danyen man a manyan tankunan matatar.
Shirin da matatar man Dangote ta yi
Wannan na zuwa ne bayan da aka samu rahotanni a jiyar Alhamis cewa matatar Dangote za ta fara aiki ba da jimawa ba, The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote ya taba cewa matatar za ta fara aikin tace gangar danyen mai dubu 350 a kowacce rana (bpd).
A sanarwar, kamfanin ya ce za a kaddamar da fara aikin matatar da wannan ganga miliyan daya da ta karba, yayin da za ta sake karbar wasu ganga miliyan biyar nan gaba.
Matsalar mai ta kare a Najeriya?
Matatar man ta ce ta na sa ran zuwan jiragen ruwa hudu daga kamfanin mai na Najeriya (NNPC) nan da mako uku, wanda zai sauke masu karin danyen mai.
A cewar matatar:
"Muna fatan idan muka gama karbar kaya daga NNPC da ExxonMobil, za mu iya sarrafa ganga dubu 350 kowacce rana, amma za mu fara fitar da man dizal, man jiragen sama da LPG, daga baya ne za mu fitar da fetur (PMS).
"Fara aikin matatar zai taimaka wajen kawo karshen matsalolin da Najeriya ke fuskanta a waduwar mai, da ma sauran kasashen Afrika ta Yamma."
Matatar man Waltersmith ta fara aiki a Imo
A wani labarin, Heineken Lokpobiri, karamin ministan albarkatun man fetur, ya yabawa matatar mai ta WalterSmith Modular bisa cimma muradun kasar kan samar da makamashi.
Matatar man wacce ta ke a Ibigwe, karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo tana samar da lita miliyan 600 na kayayyaki iri daban-daban.
Asali: Legit.ng