Nasara: Yan Bindiga da Yawa Sun Mutu Yayin da Sojoji Suka Daƙile Hare-Hare Biyu a Jihar Arewa

Nasara: Yan Bindiga da Yawa Sun Mutu Yayin da Sojoji Suka Daƙile Hare-Hare Biyu a Jihar Arewa

  • Sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile hare-haren yan bindiga biyu, sun halaka uku daga ciki a kauyukan jihar Zamfara
  • Rundunar Operation Hadarin Daji ta bayyana cewa dakarunta sun kwato makamai yayin artabu da ƴan ta'addan
  • Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin yankunan da ake fama da yawaitar hare-haren yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Dakarun sojin Operation Hadarin Daji sun daƙile harin ƴan bindiga a kauyen Danjibga da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Haka kuma rundunar ta haɗin guiwa ta kuma dakile yunƙurin barnar amfanin gona a kauyen Faru dake karamar hukumar Maradun duk a jihar ta Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin farmaki kan tawagar ƴan kwallon jihar APC, sun yi musu mummunar illa

Sojoji sun murkushe yan bindiga uku a Zamfara.
Yan bindiga sun bakunci lahira yayin da sojoji suka dakile hari a Zamfara Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Yayin artabu, yan bindiga uku sun bakunci lahira yayin da dakarun suka samu nasarar kwato bindigu kirar AK-47 guda uku, alburusai da kuma baburan ƴan ta'addan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Yadda lamarin ya faru

Ya ce a ranar 7 ga watan Disamba, sojojin hadin gwiwa na Operation Hadarin Daji sun dakile wani harin ta’addanci da aka kai kauyen Danjibga da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

A cewarsa, bayan doguwar musayar wuta, 'yan bindiga biyu suka sheka barzahu yayin da sauran suka gudu ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Kyaftin Ibrahim ya ce:

“Sojojin sun kwato bindigu kirar AK-47 guda biyu, magazine guda ɗaya, da babur daya yayin da suka bi sawun ‘yan ta’addan."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari ƙauyuka 4 a Arewa, sun kashe rayuka da yawa

Sojoji sun kara dakile wani harin

Haka zalika, a wannan rana, an sake samun wata arangama tsakanin sojoji da ‘yan ta’adda a kauyen Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

A cewarsa, Sojoji sun yi artabu da yan bindigan ne bayan samun bayanai kan yadda suka lalata gonakin jama'a a yankin kauyen Faru, Leadership ta rahoto.

Ya ci gaba da cewa:

"Dakarun soji sun fafata da maharan wanda daga ƙarshe dole suka tsere domin tsira da rayuwarsu. A musayar wutan an kashe ɗan bindiga ɗaya kuma an kwato bindiga, alburusai da babur."

Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto

A wani rahoton na daban Yan bindiga sun kai sabbin hare-hare wasu ƙauyaka a jihar Sakkwato sun kashe mutane akalla 9 ranar Litinin zuwa Talata.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kuma sace wasu da mutane da dama har da mata da kananan yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262