Shugaba Tinubu Ya Ɗauki Mataki Kan Sojoji da Suka Jefa Bam a Taron Musulmi
- Bola Ahmed Tinubu ya lashi takobin hukunta duk wanda aka gano da laifi a harin bama-baman ƙauyen Tudun Biri
- Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne ta bakin Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tawaga zuwa Kaduna don jajantawa waɗanda abun ya shafa
- Ya ce Gwamnatin Tarayya zata ɗauki matakan kare al'umma a koƙarinta na kawar da ayyukan ta'addanci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa duk wanda aka kama da hannu a harin bama-baman da aka kai kauyen Kaduna zai ɗanɗana kuɗarsa.
Shugaba Tinubu ya ce duk wanda aka gano yana da hannu a harin bama-baman wanda ya yi ajalin mutane sama da 100 a kauyen Tudun Biri a Kaduna, za a hukunta shi.
Tinubu ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ɗauki ɗawainiyar kula da lafiyar waɗanda suka jikkata a karkashin shirin 'Folako Initiative' wanda za a fara a wannan watan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, ƙauyen Tudun Biri zai zama gari na farko da gwamnati zata fara ginawa a sabon tsarin da ta ɓullo da shi, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
Ya yi wannan furucin ta bakin mataimakinsa, Kashim Shettima, jim kaɗan bayan ya kai ziyara asibitin Barau Dikko domin jajantawa waɗanda lamarin ya shafa da ta'aziyya.
Matakan da gwamnatin tarayya za ta ɗauka
Shettima ya ce gwammatin tarayya ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen yaƙi da yan ta'adda a faɗin sassan kasar.
A rahoton The Nation, Mataimakin shugaban ƙasar ya ce:
"Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya turo mu domin mu jajantawa al'ummar jihar Kaduna bisa wannan ibtila'i mara daɗi. Manyan mutanen da ke tare dani shaida ne na yadda lamarin ya girgiza shugaban ƙasa."
"Muna mai tabbatar wa al’umma da gwamnatin jihar Kaduna cewa gwamnati za ta dauki matakan kariya da tsare mutuncin ƙasar nan."
"Za a dauki matakan da ya dace domin dakile faruwar irin haka nan gaba. Gwamnati za ta gano tushen lamarin kuma duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi yadda ya kamata."
Shettima ya ziyarci Kaduna kan kuskuren harin bam
A wani rahoton kuma Kashim Shettima da wasu manyan kusoshin gwamnati sun ziyarci Kaduna kan harin bama-baman soji a taron masu Maulidi.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai ziyarci ƙauyen Tudun Biri domin jajantawa waɗanda harin ya shafa.
Asali: Legit.ng