Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke Abuja Kan Kujerar Wike
- Wasu rukunin masu zanga-zanga sun sake mamaye Abuja domin yin zanga-zanga a kan neman a tsige Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya
- Daruruwan mutanen sun lissafa nasarorin da ministan ya samu cikin dan kankanin lokaci da kama aiki
- Hakan na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 bayan wata kungiyan yan Abuja sun yi zanga-zanga da neman a tsige Wike a matsayin ministan birnin tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, na ci gaba da fuskantar rikicin siyasa tun bayan da Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shi mukami bayan ya mara masa baya a zaben shugaban kasa na 2023.
A ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, wasu mazauna Abuja sun yi tururuwa da yawansu don zanga-zanga a kan nadin nasa, suna zarginsa da badakalar filaye sannan suka bukaci Shugaban kasa Tinubu da ya tsige shi.
Kungiyar ta yi zargin cewa Abuja ta shiga idon duniya tun bayan da Wike ya kama aiki a matsayin ministan Abuja, inda ta kara da cewa bai kamata mutane irinsa su kasance cikin ajandar sabunta fata ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma a safiyar ranar Alhamis, 7 ga watan Disamba, wata kungiyar yan Abuja ta gudanar da zanga-zanga kan kira da ake na neman a tsige Wike a matsayin ministan birnin tarayya, cewa nadinsa ya kawo gagarumin ci gaba a babban birnin Najeriya.
Sun lissafa nasarorin da tsohon gwamnan na jihar Ribas ya samu tare da yin kira ga Shugaba Tinubu da ya bar Ministan ya ci gaba da aikinsa.
Kungiyar ta ce zargin cewa Wike na lalata ajandar sabunta fata na Shugaba Tinubu, cewa yana da hannu a kwace filaye da sauransu ba gaskiya bane.
Sun ce tun bayan da Wike ya kama aiki a matsayin minista, ya yi nasarar hada kai da hukumar kula da harkokin kamfanoni (CAC) tare da fallasa wasu kamfanoni sama da 100 da suke damfarar mutane.
Kalli bidiyon a kasa:
An yi zanga-zanga kan Wike a Abuja
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa dubban mazauna garin Abuja su ka shirya zanga-zanga domin ganin Nyesom Wike ya sauka daga kujerar da yake kai a yau.
Sahara Reporters ta ce masu zanga-zangar sun yi kira ne ga Nyesom Wike ya yi murabus daga matsayinsa na Ministan birnin Abuja.
Asali: Legit.ng