Tudun Biri: Ƙungiyar MURIC Ta Maida Zazzafan Martanin Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna

Tudun Biri: Ƙungiyar MURIC Ta Maida Zazzafan Martanin Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna

  • Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta maida zazzafan martani kan kisan da sojoji suka yi wa masu Maulidi a jihar Kaduna
  • MURIC ta bukaci Gwamnatin Bola Tinubu ta gudanar da bincike mai zurfi kuma a hukunta duk wanda aka kama da hannu a harin Tudun Biri
  • Farfesa Akintola ya ce bai kamata sojoji su juya akalar abin harinsu kan fararen hula ba, wannan rashin kwarewa ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Kungiyar nan mai fafutukar kare hakkin musulmai a Najeriya 'Muslim Rights Concern (MURIC)' ta maida martani kan bama-baman da sojoji suka jefa wa masu Maulidi a Kaduna.

MURIC ta yi magana kan harin da aka kai kan masu Maulidi.
MURIC ta bukaci FG ta gudanar da cikakken bincike kan kisan Musulmai a Kaduna Hoto: MURIC, NAF
Asali: Twitter

Kungiyar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hanzarta gudanar da bincike kan harin bama-baman jirgin soji, wanda ya halaka Musulmai aƙalla 120 a kauyen Tudun Biri.

Shugaban MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Sanata ya faɗi matakin da zasu ɗauka domin tabbatar da adalci kan kisan masu Maulidi

Sanarwan ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jirgin sojoji ya kashe mutane 120 da ba su ji ba kuma ba su gani ba a kauyen Tudun Biri, karamar hukumar Igabi a Kaduna ranar Lahadi."
"Mutanen suna tsaka da murnar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW lokacin da mummunan ibtila'in da afka musu."
"Duk da rundunar sojojin ƙasa ta ɗauki laifin, muna Alla wadai da kisan mutanen kauyen da ba ruwansu, wannan abu ya nuna rashin kulawa da ƙwarewar sojoji."

Abinda muke bukatar FG ta yi - MURIC

Shugaban MURIC ya ƙara da cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da duk mai hannu a lamarin ya girbi abin da ya shuka.

A rahoton The Cable, Farfesa Akintola ya ci gaba da cewa:

"MURIC na buƙatar a yi bincike mai zurfi kan ibtila'in, duk wanda aka samu da hannu a kisan gillar da aka yi wa wadannan mutanen Musulmi wadanda ba su ji ba ba su gani ba, a hukunta shi."

Kara karanta wannan

Ana jimamin harin sajoji kan masu mauludi, dakarun sojoji sun sheke masu ba yan bindiga bayanai

"Kuma muna neman a biyaɓdiyyar rayukan da aka rasa da dukiyoyi aka lalata a wannan harin na rashin tunani."
"Rayuwa abu ne mai daraja kuma bai kamata sojoji su mayar da fararen hula marasa laifi su zama abin kaiwa farmaki da makaman yaƙi ba."

Sheikh Ɗahiru Bauchi ya yi magana

A wani rahoton na daban Sheikh Ɗahiru Bauchi ya buƙaci Bola Ahmed Tinubu ya tabbata an hukunta sojojin da suka kai harin bam kan masu Maulidi a Kaduna.

Fitaccen Malamin ya aike da saƙon ta'aziyya ga al'ummar Musulman Najeriya da na duniya kan wannan ibtila'i da ya ci rayuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262