Kaico: Shekara Biyar da Ritaya, Sufetan ’Yan Sanda Ya Koma Barace-Barace a Titi
- Labarin wani tsohon sufetan 'yan sanda da ya koma yin bara shekaru biyar bayan ritaya ya ja ra'ayin jama'a
- Mr Sunday Ogwo Okpalle ya kasance jami'in dan sanda na tsawon shekara talatin da biyar, inda ya yi aiki a jihar Niger
- Sai dai, tsadar rayuwa da sauyin yanayi ya tilasta shi yin bara a titunan jihar don samun abin da zai ciyar da iyalinsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Niger - Sauyin rayuwa ya sa wani Sunday Ogwo Okpalle, sufetan 'yan sanda mai anini biyu da ya koma wa mabaraci a kan titunan jihar Niger..
Sunday Okpalle, ya shafe kusan rasuwarsa yana aikin dan sanda, matsayin mai bayar da hannu a kan titi a jihar.
A safiyar ranar Talata, wakilin jaridar Punch ya ci karo da Okpalle, wanda ke bin masu motoci, Keke Napep da 'yan acaba yana rokon kudin da zai ci abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ku taimake ni ko na sami na cin abinci," ya ke nanata wa masu ababen hawan, wadanda ba sa ko kula shi.
Yayin da wasu suka ba shi taimako daga abin da suke da shi, wasu kuma sukan ce:
"Ku kyale shi, haka yake bara a nan kullum, ba ya ko gajiya."
Takaitaccen bayani kan rayuwar Mr Okpalle
Da ya zanta da wakilin Punch, ya shaida masa cewa tsananin rayuwar da ya shiga ne ya tilasta shi yin bara, rashin yin hakan na iya saka shi kwana da yunwa.
Batu kan fansho da ya ke karba kuwa, ya tabbatar da cewa ana tura masa naira dubu talatin ne kuma kudin na zuwa ne a kurarren lokaci.
"Rayuwa ba ta yi mun kyau ba, shekara biyar da yin ritaya yanzu, ina da yara biyar da mata daya, amma sai na yi bara muke cin abinci.
"A lokacin da nake aiki, nakan samu naira dubu uku zuwa hudu kafin na tashi aikin ranar, amma yanzu ko sisi bana samu."
Me ya faru da kudin giratutin Mr Okpalle?
A cewar Mr Okpalle, kamar yadda Legit ta ruwaito, inda ya kara da cewa:
"Sai da na yi shekara daya da rabi sannan na samu naira miliyan 1.7 na giratuti madadin miliyan 6. Haka na hakura, daga nan duk wata ake tura mun naira dubu talatin kudin fansho.
"Kudi sun zo sun kare saboda dawaniyar karatun yara da hidimar gida, karshe dai dole na dawo yin bara don ciyar da iyalina."
A karshe ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka ta biya sa karashen kudin giratutinsa ko ya samu ya farfado daga wannan bakin talaucin da ya ke ciki.
Wata daya: ’Yan sanda sun damke masu laifi 130 a Katsina
A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta sanar da nasarar da dakarunta suka samu na afke masu laifi 130 a jihar Katsina
Daga cikin wadanda aka kama akwai 'yan fashi 38, masu kisan kai 16, da sauransu, kuma ta kubutar da mutum 69, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng