Abinda yasa ƴan Najeriya ke kwana da yunwa duk da noman abinci da ake yi, Nanono

Abinda yasa ƴan Najeriya ke kwana da yunwa duk da noman abinci da ake yi, Nanono

  • Ministan noma da bunkasa karkara, Alhaji Muhammad Nanono, ya bayar da dalilan da suka sa har yanzu wasu ‘yan Najeriya suke kwana da yunwa duk da ana noma kayan abinci
  • Ministan ya yi wannan jawabin ne a wani taro da suka yi a Abuja inda yace hakan yana faruwa ne saboda ba su da isasshen kudin da za su siya abincin
  • Ya danganta hakan da matsalar rashin ayyukan yi wanda hakan yake dakatar da mutane daga samun kudaden siyan abinci, biyan kudin haya da na makarantu da sauransu

FCT, Abuja - Ministan noma da bunkasa karkara, Alhaji Muhammad Nanono, ya bayar da kwararan dalilan da suke janyo wa ‘yan Najeriya kwana da yunwa duk da tarin noman da ake yi a kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan ya yi wannan furucin ne a wani taro da suka yi a Abuja, inda yace hakan yana faruwa ne saboda basu da isassun kudaden da za su siya abinci.

Kara karanta wannan

Ya zama dole ku bayyana mana su wanene 'Unknown Gunmen', Sarkin Musulmi ya fada wa Hukumomin Tsaro

Abinda yasa ƴan Najeriya ke kwana da yunwa duk da noman abinci da ake yi, Nanono
Abinda yasa ƴan Najeriya ke kwana da yunwa duk da noman abinci da ake yi, Nanono. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya danganta matsalar da rashin ayyukan yi wanda hakan yake dakatar da mutane daga siyan abinci, biyan haya da kudin makaranta. Ya ce kasar nan tana fuskantar kalubale.

Ban dade da haduwa da wasu matasa ba wadanda suke sarrafa kayan abinci da kuma bunkasa injina, kuma wannan ne muka fi bukata a kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matsawar ba mu yi gyara ba, talauci zai cigaba da yawaita.
Idan bamu mayar da hankali wurin ganin mun kawo karshen rashin aikin yi ga matasa ba, babu wani cigaban da za mu samu. Dole a alakanta harkar noma da ma’aikatu,” a cewarsa.

Gwamnatin tarayya za ta cigaba da samar da sababbin hanyoyin da za su bunkasa harkokin noma.

Idan muka mayar da hankali ga sabon tsarin NATIP, zai taimaka mana wurin samar da hanyar bunkasa hanyoyin samun kudi ta harkokin noma, za mu rage shigo da kayan abinci kasar nan sannan zai taimaka ta yadda noma za ta dinga samar wa Najeriya kudaden shiga,” a cewarsa.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro: Idanun masu kula da CCTV ta NDA biyu yayin da aka kai hari

Ya koka a kan yadda har yanzu Najeriya take shigo da kayan abinci masu yawa don haka noma bata samar da kudaden shiga ga kasar nan.

A cewar ministan, ta hanyar bunkasa noma ne kadai zai taimaka wurin wadata Najeriya da kayan abinci sannan a fitar dasu har kasashen waje, Daily Trust ta ruwaito.

Gurguwar hanya ake bi wurin samar da abincin kasar nan

Sai dai karamin ministan noma da bunkasa karkara, Mustapha Shehuri, ya bayyana tsarin samar da abincin kasa rnan a matsayin gurguwar hanya.

Ya samu wakilcin darektan sashin aikin noma na tarayya, Hajiya Karima Babangida. Shehuri ya ce an shirya taron ne musamman saboda taimakawa wurin farkar da ‘yan Najeriya, don ganin an yi gyara wurin bunkasa tattalin arzikin noma da samar da isasshen abinci.

Ya ce an shirya ma’aikatar ne musamman don kawo gyara a kan kawo karshen samar wa da ‘yan Najeriya hanyar samun abinci mai kyau, lafiya da kuma inganci.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

Yanzu haka ana kokarin ganin an samar da kayan abinci ta hanyar noma don samun kubutaccen abinci kuma tsaftatacce a bangarori daban-daban da ke kasar nan,” a cewarsa.

Ya kara da cewa noma zai iya zama hanyar kawo karshen yunwa, rashin ayyuka da fatarar da ke addabar kasar nan.

Cikar Najeriya shekaru 61: FG ta kafa kwamitin mutum 12 domin shirye-shirye

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta rantsar da kwamitin mutane 12 da suka hada da ministoci domin tsara yadda shagalin bikin cika murnar shekaru 61 da samun 'yancin kan kasa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Najeriya za ta cika shekaru 61 a ranar 1 ga watan Oktoba.

A yayin rantsar da kwamitin a ranar Alhamis a Abuja, sakataren gwamnatin tarayya, SGF Boss Mustapha, ya ce hikimar nan ta biyo bayan bukatar fara shirin shagalin da wuri domin samun sakamako mai kyau, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel