Zamu Tabbatar da An Yi Wa Mutanen da Aka Kashe a Kaduna adalci, Sanata

Zamu Tabbatar da An Yi Wa Mutanen da Aka Kashe a Kaduna adalci, Sanata

  • Sanata Sunday Marshall Katung ya ce zasu tabbata an yi wa mutanen da harin bam ɗin sojoji ya shafa adalci
  • Katung, Sanata mai wakiltar Kaduna ta kudu ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu a kauyen Tudun Biri
  • Haka nan Sanata Hussaini daga jihar Jigawa ya aike da saƙon ta'aziyya ga abokin aikinsa na Kaduna da tsakiya da mutanen kauyen

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ƙaduna - Sanatan Kaduna ta kudu, Sunday Marshall Katung, ya ce zai haɗa kai sauran mambobin majalisar tarayya wajen nemawa mutanen da aka kashe adalci.

Sanatan Kaduna ta kudu ya maida martani.
Zamu Tabbatar da An Yi Wa Mutanen da Aka Kashe a Kaduna adalci, Sanata Hoto: Kaduna State Map
Asali: UGC

Sanatan ya bayyana cewa zasu aiki wajen ganin cewa dukkan dangogin da harin bama-baman soji ya shafa a taron Maulidi a Tudun Biri, an musu adalci bisa kisan ƴan uwansu.

Kara karanta wannan

Ana jimamin harin sajoji kan masu mauludi, dakarun sojoji sun sheke masu ba yan bindiga bayanai

A ranar Litinin, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta fito ta karɓi laifin cewa jami'anta ne suka yi ruwan bama-baman bisa kuskure, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tudun Biri da ke gundumar Afaka a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, kuma zuwa yanzu sama da mutum 100 suka mutu.

A wata sanarwa da ya fitar domin jajantawa al’ummar jihar Kaduna da waɗanda abin ya shafa, Sanata Katung ya ce za su tabbatar an kula da wadanda suka tsira.

“Wannan lamari abin takaici ne da kuma koma baya ga sabbin hare-haren da ake kaiwa ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a yankin, jihar Kaduna da ma kasa baki daya,” in ji shi.

Sanatan Jigawa ya yi ta'aziyya

Haka kuma, Sanata Babangida Hussaini mai wakiltar Jigawa ta arewa maso yamma, ya yi ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa a Kaduna.

Kara karanta wannan

Sheikh Ɗahiru Bauchi ya yi martani kan kisan masu Maulidi a Kaduna, ya aike da saƙo ga Tinubu

A saƙon ta’aziyya da ya aike wa Sanata Lawal Adamu Usman (Kaduna ta tsakiya) da al’ummar mazabarsa, Hussaini ya ce ya labarin ya yi matuƙar girgiza shi.

A cewarsa, abin takaici ne yadda sojoji suka kai harin bam bisa kuskure kan mutanen kauyen da ba su ji ba ba su gani ba, cewar Channels tv.

Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya isa Abuja, babban birnin tarayya bayan halartar taron sauyin yanayi na majalisar ɗinkin duniya a Dubai.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kiraye-kiraye ya ɗauki mataki kan kisan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262