“Ban Ji Dadi Ba”: Tinubu Ya Magantu Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna, Ya Bayar da Wani Umurni
- Biyo bayan wani harin bam da rundunar soji ta kai kan wasu masu maulidi a Kaduna, Shugaba Tinubu ya bayar da umurnin yin bincike
- Da ya ke jajantawa al'ummar garin Tudun Biri da lamarin ya shafa, Tinubu ya kuma nuna kaduwarsa matuka kan mutuwar mutanen
- Shugaban kasar ya kuma umurci a bai wa wadanda suka tsira daga harin duk wata kulawa da suke bukata ta asibiti yayin da ake bincike kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan waki'ar da ta fadawa wasu masu maulidi a karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.
A ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023, rundunar soji ta sakar wa masu maulidin bama bamai, inda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Shugaban kasar a cikin wata sanarwa daga mai tallafa masa ta fuskar watsa labarai, Chief Ajuri Ngelale, ya jajantawa iyalan garin Tudun Biri, bisa wannan iftila'i.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Tinubu ya ce kan harin da aka kai wa masu maulidi?
Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin "abin daga hankali mai sanya radadi a zuciya", inda ya nuna kaduwarsa kan wannann babban rashi da al'ummar garin suka yi.
Sanarwar ta kuma kara da ce:
"Shugaban kasar ya bayar da umurni a gudanar da bincike kan lamarin, tare da yin kira ga al'umma da su kwantar da hankalinsu don bai wa jami'an tsaro damar gudanar da aikinsu kanlamarin.
"Haka zalika shugaban ya umurci a bai wa wadanda suka tsira daga harin kyakkyawar kulawa ta kiwon lafiya, yayin da kuma ya yi addu'a ga wadanda suka riski ajalinsu a harin."
Rundunar sojin sama ta yi martani kan zargin kai harin bam kan masu Maulidi a Kaduna, ta roki jama'a
Sanarwar wacce Legit Hausa ta ci karo da ita a shafin ofishin mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar kafofin sada zumunta, an fitar da ita ne a safiyar ranar Talata, 5 ga watan Disamba, 2023.
Ga binda sanarwar ke cewa:
An nemi Kotun Koli ta tsige Tinubu daga shugaban kasa
A wani labarin kuma, an nemi Kotun Koli ta tsige Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa kundin dokar da ya ce 'Lis Pendens'.
Jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP) ta bayyana cewa kundin dokar Lis Pendens ya ayyana zaben shugaban kasar 2023 matsayin 'haramtacce', kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng