Zargin Maita: Yan Sanda Sun Kama Mutum 2 Kan Kashe Dan Uwansu da Yunwa a Nasarawa
- Jami'an yan sandan jihar Nasarawa sun kama wasu maza biyu kan zargin horar da dan uwansu da yunwa har lahira
- Mutanen biyu da ake zargi sun daure Mohammed Sani mai shekaru 35 sannan suka hana shi abinci har ya mutu kan zargin maita
- Sai dai kuma, mazan da aka kama sun karyata aikata laifin, suna masu cewa su dai sun shiga sahun masu binne Sani ne bayan an gano gawarsa da ta rube a dakinsa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Lafia, jihar Nasarawa - Yan sanda sun kama wasu maza biyu kan zargin rufe dan uwansu mai shekaru 35, Mohammed Sani tare da horar da shi da yunwa har lahira kan zarginsa da ake yi da maita a jihar Nasarawa.
Mukaddashin kwamishinan yan sandan jihar, Shettima Muhammad, wanda ya bayyana hakan ya ce an rufe Sani a dakinsa inda aka yi masa horo da yunwa har lahira bayan an dare hannaye da kafafunsa.
Ana ci gaba da bincike don kamo sauran masu laifi, rundunar yan sanda
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, CP Muhammad ya ce dangin sun yi gaggawan binne gawar Sani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yan sanda sun samu labari a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba sannan cewa bincike na gudana domin kama sauran mutane da ke da hannu a laifin.
Ya kara da cewar mutane biyun da aka kama sun bayyana cewa su dai sun shiga sahun masu binne Sani ne bayan an gano gawarsa da ta rube a dakinsa, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
Zargin maita: Matashi ya kashe kawunsa
A wani labari makamancin wannan, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa wata kotun majistare ta aika wani matashi zuwa magarkama kan zarginsa da halaka kawunsa a jihar Adamawa.
Wanda ake zargin mai suna John Clarkson mai shekaru 42 ya sheke kawun nasa ne saboda zargin maita.
Kotun majistare da ke Yola karkashin jagorancin Mai Shari'a, Alheri Ishaku ita ta yanke wannan hukunci kan wannan tuhuma da ake masa. Ta umarci tsare Clarkson dan asalin kauyen Dumna Zarbu da ke karamar hukumar Guyuk a jihar.
Asali: Legit.ng