Shugaban Masu Rinjaye: Majalisar Jihar Arewa Ta Yi Sabbin Nade-Nade Guda 3
- Bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara na korar wasu 'yan majalisu a jihar Nasarawa, majalisar dokokin jihar ta yi sabbin nade-nade guda uku
- Kakakin majalisar jihar Danladi Jatau ya sanar da nade-naden da suka hada da na shugaban masu rinjaye da mataimakinsa, sai kuma bulalar majalisar
- A cewar kakakin majalisar, nadin ya zama wajibi la'akari da cewa majalisar ba za ta iya gudanar da aiki ba tare da mukaman ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lafia, jihar Nasarawa - Sabon kakakin malisar jihar Nasarawa, Danladi Jatau ya sanar da nadin wasu manyan mukamai guda uku a zauren majalisar.
Sabbin nade-naden da aka yi sun hada da Suleiman Yakubu Azara daga mazabar Awe ta Kudu karkashin APC matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar.
Dalilin yin sabbin nade-naden
Sai kuma Abel Yakubu Bala matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye, da kuma Ibrahim Aliyu matsayin mataimakin bulalar majalisar, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan nade-nade ya biyo bayan wani hukunci da kotu ta yanke na sake gudanar da zabe a mazabar tsohon shugaban masu rinjaye, Mohammed Omadefu mai wakiltar mazabar Keana.
Kakakin majalisar ya yi nade-naden ne a zaman majalisar na ranar Litinin a garin Lafia, inda ya ce majalisar ba za ta iya aiki ba tare da shugaban masu rinjaye, mataimakinsa da kuma mataimakin bulalar majalisar.
Me kakakin majalisar ya ce kan nade-naden?
Ya ce:
"Idan za ku tura a ranar 1 ga watan Disamba, aka zabe ni matsayin kakakin majalisa, hakan ya sa babu kowa kan tsohuwar kujerata ta mataimakin shugaban masu rinjaye da shugaban kwamitin ilimi.
"Haka zalika, bisa hukuncin Kotun Daukaka Kara, babu kowa yanzu a kujerar shugaban masu rinjaye.
Jatau ya kara da cewa:
"Da wannan na sanar da nadin Hon. Suleiman Yakubu Azara matsayin sabon shugaban masu rinjaye, da Hon. Abel Yakubu Bala matsayin mataimaki.
"Sannan na nada Hon. Ibrahim Nana matsayin sabon mataimakin bulalar majalisar. Wadannan matakan za su fara aiki nan take."
Kakakin majalisar ya kuma sanar da Hon. Abel Yakubu Bala matsayin sabon shugaban kwamitin ilimi na majalisar.
Gwamnatin Katsina ta koka kan matsalar tsaro
A wani labarin, gwamnatin jihar Katsina ta doka kan yadda wasu makarantu a jihar suka koma mafakar 'yan ta'adda.
Gwamnan jihar, Umar Dikko Radda ya ce ayyukan ta'addanci a jihar sun jawo rufe makarantu da dama, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng