Auren Diyar Sani Abacha da Gwamna Mai Mala Buni Ya Mutu
- Zaman aure ya ƙare tsakanin Gwamna Mai Mala Buni na juhar Yobe da tsohuwar matarsa Gumsu Sani Abacha
- Gumsu wacce ɗiya ce a wajen tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Sani Abacha ta tabbatar da mutuwar auren na ta gwamnan a wata wallafa a X
- Majiyoyi na cikin gida sun tabbatar da cewa auren na Mai Mala da Gumsu ya mutu ne watanni shida da suka wuce
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Auren da ke tsakanin Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da Gumsu Sani Abacha ya mutu.
Ɗiyar marigayi shugaban mulkin soja Sani Abacha ta bayyana rabuwar auren ta yayin da take mayar da martani ga wani mai sharhi da ya kira ta da “uwargidan gwamna” a kan shafinta na X @G_sparking a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba.
Kaduna: Rundunar Sojin Ƙasa ta ɗauki laifi, ta faɗi gaskiyar abinda ya jawo jefa bam a taron Maulidi
Gumsu ta sanya hotunanta tare da taken kalmomi biyu, “sakewa… kwatar ƴanci” a ranar Lahadi, wanda ya jawo ɗaruruwan martani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta cikin gida ta kuma tabbatar wa da jaridar Daily Nigerian cewa auren ya mutu “watanni da suka gabata"
Yaushe aka yi bikin aurensu?
A ranar 14 ga watan Afrilu, 2021, Buni ya auri Gumsu Abacha mai shekaru 45, kuma ya biya zinari 24 a matsayin sadaki.
An daura auren ne a gidan babban yayanta, Mohammed Abacha a Abuja, wanda ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗs shugaban hukumar kwastam ta Najeriya a lokacin, Hameed Ali.
Sauran sun haɗa da tsohon kwamishinan ƴan gudun hijira, Bashir Garba-Lado, Sheikh Aminu Daurawa, ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2023, Yakubu Lado Dan-Marke, da dai sauransu.
A baya Gumsu ta auri wani hamshaƙin attajirin ɗan ƙasar Kamaru mai suna Bayero Mohamadou, amma auren wanda ya shafe shekara 20 ya mutu a shekarar 2020.
Magidanci Ya Maka Matarsa a Kotu
A wani labarin kuma, wani magidanci ya maka matarsa a gaban kotun shari'ar musulunci kan zargin yin aure bisa aure.
Magidancin mai suna Yakubu Nuhu wanda yake zaune a ƙasar Saudiyya, ya buƙaci kotun da ta raba auren da matarsa ta yi a kan nasa.
Asali: Legit.ng