Abin da Yasa Tibunu Bai Yi Jawabinsa Ba a Taron COP28 Kamar Yadda Aka Shirya

Abin da Yasa Tibunu Bai Yi Jawabinsa Ba a Taron COP28 Kamar Yadda Aka Shirya

  • An gano babban dalilin da ya sa shugaban Najeriya bai gabatar da jawabi ba a taron COP28 da ke gudana a Dubai
  • Ministan harkokin kasashen waje ya ta'allaka rashin jawabin shugaban da cewa "Tinubu ya damu da aiki a kasa ba yawan magana ba"
  • Sai dai wani bincike ya nuna cewa shugaba Tinubu ya fice daga dakin taron ne don ganawa da wani shugaban kasa, abin da bai yiyu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kasar Dubai - Bisa al'ada ta taron dumamar yanayi na majalisar dinkin duniya da aka fi sani da COP, ana ba shugabannin kasashe damar gabatar da jawabai kwanaki biyu da fara taron.

Duka jawaban shugabannin kasashen kan ta'allaka ne kan hanyoyi, kudurori da matakan da kasashen su ke bi ko za su bi wajen magance matsalar dumamar yanayi.

Kara karanta wannan

Akwai alheri 1: Shugaba Tinubu ya gana da shugaban UAE, hotuna da bayanai sun bayyana

Tinubu a taron COP28
Fadar shugaban kasa ta magantu kan dalilin Tinubu na gaza yin jawabi a taron COP28. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Me ya faru a taron COP26 da COP27?

A taron COP26 da ya gudana a Birtaniya a shekarar 2021, shugaban Najeriya a wancan lokaci Muhammadu Buhari ya ce Najeriya za ta kawo karshen gurbacewar iska kafin 2060.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a taron COP27 da ya gudana a Masar, Buhari bai halarci taron ba, sai dai ya samu wakilcin ministan muhalli Mohammed Abdullahi, wanda ya yi jawabi madadin Buhari.

An tsara cewa shugabannin kasashe za su gabatar da jawabi a ranar 1 da 2 ga watan Disamba a taron COP28 na wannan shekarar mai taken "Matakai don dakile dumamar yanayi a duniya".

Fadar shugaban kasa ta fadi dalilin Tinubu na gaza gabatar da jawabi a taron

Shugaba Bola Tinubu ne na 36 a jadawalin shugabannin kasashen da za su gabatar da jawabi a wannan taron, amma har rana ta daya da ta biyu ta wuce shugaban bai yi jawabi ba.

Kara karanta wannan

"Cin zabe sai an hada da rauhanai" Shehu Sani ya yi wa Doguwa martani

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Tinubu bai gabatar da jawabi ba saboda yakininsa na cewa "aiki a aikace Najeriya ke so ba wai yawan magana ba", kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Amma a rahoton jaridar The Cable ya gano wani dalili akasin ikirarin ministan, inda ta gano cewa Tinubu ya bar tadin taron misalin 4:10 na yamma don ganawa da wani shugaban kasa.

Mene gaskiyar abin da ya sa Tinubu bai yi jawabi ba?

Sai dai ganawar ba ta yiwu ba, inda kai tsaye Tinubu ya wuce dakin otel dinsa, daga bisani ya sake dawowa don sa hannu kan wata yarjejeniya da Olaf Sholz, shugaban Jamus, da nufin bunkasa samar da lantarki a Najeriya.

Domin nunawa 'yan Najeriya cewa Tinubu na dakin taron, aka aka ministan muhalli Balarabe Lawal ya zauna a kujerar shugaban kasar, duk da hakan, aka tsallake sunan shugaban a masu gabatar da jawabi.

Kara karanta wannan

Kasafin 2024: Jam'iyyar SDP ta shirya yin aiki da Tinubu don ci gaban Najeriya

Masu shirya taron sun ce shugabannin kasashe ne kawai za su iya gabatar da jawabi a zaman farko na taron, wakilai sai dai su jira zuwa rana ta tara.

Yan fansho ga Tinubu: Janye tallafin man fetur ya jefa mu mawuyacin hali

A wani labarin, 'yan fansho a Najeriya sun koka wa shugaban kasa Bola Tinubu kan halin da suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur.

Kungiyar 'yan fansho ta kasa (NUP) ta ce sun gabatar da bukata ga ministar jin kai don saka 'yan fansho a wani tallafin gwamnati, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.