Tinubu Ya Siya Hannun Jarin Atiku Na $100m a Kamfanin Intels? Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana
- A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaba Tinubu ya yi tsokaci kan cece-kucen da ake tafkawa a kan hannun jarin Atiku na dala miliyan 100 a kamfanin Intels
- Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa kawo ƙarshen kwangiloli tsakanin NPA da Intels a shekarar 2020 ya haifar da raguwar kuɗaɗen shiga da Najeriya ke samu
- Sai dai, kuma sanarwar ta Tinubu ta tabbatar da cewa Atiku ba ya da alaƙa da kamfanin INTEL a halin yanzu kuma gwamnati ba ta soke kwangilar su ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan cece-kucen da ake tafkawa a kan hannun jarin Atiku Abubakar na dala miliyan 100 a kamfanin Intels.
Daga ƙarshe Tinubu yayi magana akan hannun jarin Atiku
Fadar shugaban ƙasa a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, ta yi bayani dalla-dalla game da batun dakatar da kwangilolin da aka kulla tsakanin NPA da kamfanin Intels a shekarar 2020.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar fadar shugaban ƙasar, an dakatar da kwangilar ne saboda kuɗaɗen shiga da Najeriya ke samu a duk shekara, wanda ya ragu daga sama da dala miliyan 200 zuwa kusan dala miliyan 50 bayan soke kwangilar.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin sadarwar zamani, DOlusegun ya fitar ta shafinsa na X, a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Atiku ya sayar da hannun jarinsa na kamfanin sama da shekaru uku da suka gabata, kuma ya kamata a yi watsi da batun siyasa a lamarin.
Yanzu haka dai kamfanin na Intels ya koma mallakar kamfanin Orleal Investment Group, wanda ya mallaki hannun jarin Atiku a kan sama da dala miliyan 100.
Wane bayani fadar shugaban ƙasa ta yi?
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"An dakatar da ayyukan na Intels na wani ɗan lokaci saboda rashin iya aiki da ƙwarewa a tsakanin sabbin masu gudanar da ayyukan, wanda hakan ya yi tasiri wajen samar da kuɗaɗen shiga."
"Shugaba Tinubu, da hawansa mulki, ya sanya jami’ai da su binciko yadda kuɗaɗen shiga ke zurarewa, inda suka gano kwangilar ayyukan jiragen ruwa a matsayin hanyar da Najeriya ke rasa sama da $150m duk shekara."
"Ƙoƙarin warware rikice-rikice ya haifar da amincewa ga Intels ya dawo aiki a watan Nuwamban 2023."
"A tuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku ya riga ya sayar da hannun jarinsa na kamfanin sama da shekara uku da suka gabata, kuma duk wani batu na goyon bayan siyasa ya kamata a yi watsi da shi."
"Don haka yaudara ce a yarda da ko wanne daga cikin iƙirarin da ake yi na cewa Alhaji Atiku har yanzu yana da hannun jari a Intels ko kuma cewa Shugaba Tinubu ya mayar da kwangilar ne saboda ya sayi hannun jari a kamfanin."
Atiku Ya Magantu Kan Hannun Jarinsa Na $100m
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya fito ya yi magana kan batun cewa yana amfana da dawo da kwangilar da ke tsakanin kamfanin Intels da gwamnatin tarayya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni ya riga da ya siyar da hannun jarinsa na $100m a kamfanin Intels.
Asali: Legit.ng