Akwai Alheri 1: Shugaba Tinubu Ya Gana da Shugaban UAE, Hotuna da Bayanai Sun Bayyana
- A wani gagarumin yunkuri kawo ci gaba, shugaba Tinubu ya gana da Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa
- Taron wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, an yi shi ne da nufin karfafa dankon zumunci tsakanin Najeriya da UAE
- Tinubu ya bayyana irin nasarorin da aka samu a tattaunawar da suka yi tare da jaddada aniyarsu ta fadada alaka tsakanin kasashen biyu
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Dubai, UAE – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata muhimmiyar ganawa da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba.
Shugaban ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X dauke da hotunan yadda ganawar ta kasance.
Shugaba Tinubu ya wallafa cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun yi wata ganawa mai muhimmanci da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a yau, wanda zai karfafa alaka mai karfi tsakanin Najeriya da UAE da kuma kudurinmu na fadada alaka tsakanin kasashen biyu."
Su wa ke tare da Tinubu?
Kamar yadda aka gani a hotunan, Tinubu na tare da ma ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da ministan ma'adanai, Dele Alake, da wasu manyan jami'an gwamnati.
Ganawar ta Lahadi ta zama ta biyu mafi muhimmanci da Shugaba Tinubu ya yi tun bayan da ya isa Dubai a wannan tafiyar.
Tun da farko, shugaban ya tashi daga Najeriya zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa ne domin halartar taron kolin yanayi na COP28 da aka shirya gudanarwa a ranakun 1 da 2 ga watan Disamba, 2023, mai taken "Unite, Act, and Deliver".
Tinubu ya kinkimi mutane zuwa Dubai
A duk cikin kasashen Afrika da ke halartar taron COP28 da aka shirya a Dubai a kasar UAE, Najeriya ta fi kowa yawan tawaga.
Bayanan da aka samu daga hukumar UNFCCC ta majalisar dinkin duniya ya nuna Najeriya ta dauki mutum fiye da 1, 400 zuwa taron.
A duk Duniya, The Cable ta ce Najeriya ce ta uku – bayan kasar UAE inda ake taron sai kuma Brazil masu mutum 4,409 da 3,081.
Asali: Legit.ng