Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Lokacin Da Za Ta Biya Bashin Wata 9 na N-Power

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Lokacin Da Za Ta Biya Bashin Wata 9 na N-Power

  • Mambobin zubin farko da na uku (Batch B da C) da suka ci gajiyar shirin N-Power na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na cigaba da neman a biya su haƙƙoƙinsu
  • Legit.ng ta fahimci cewa, wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin na jiran alawus na watanni tara
  • An tura waɗanda suka ci gajiyar N-Power zuwa makarantu (N-Teach), asibitoci (N-Health), da cibiyoyin noma (N-Agro) kuma suna samun N30,000 duk wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara biyan bashin watanni tara ga waɗanda suka ci gajiyar shirin N-Power da suka kasance cikin shirin.

Gwamnatin tarayya, ta hanyar National Social Investment Programs (NASIMS), ta ce kwanan nan za a biya bashin N-Power idan an kammala aikin sake fasalin shirin da ake yi.

Kara karanta wannan

An bayyana dalili 1 da ya hana Atiku komawa Dubai da zama

FG za ta biya bashin N-Power
Gwamnatin tarayya za ta biya bashin wata tara na N-Power Hoto: Nasimsng, Npower
Asali: Facebook

N-Power ta fitar da sabbin bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatar kula da jin ƙai da kawar da fatara ce ke aiwatar da wannan shirin a ƙarƙashin jagorancin Betta Edu.

NASIMS ta bayyana cewa babban maƙasudin dakatar da shirin na wucin gadi shi ne magance duk wani abu da ya shafi masu cin gajiyar shirin kai tsaye.

NASIMS ta rubuta a shafinta na Facebook cewa:

"Za a fara biyan bashin alawus-alawus na Npower na watanni 9 bayan kammala sake fasalin shirin da ake yi."

Sakamakon dakatarwar na wucin gadi na shirin don yin gyara da bincike, an kwato kudade daga masu biyan kuɗin na baya.

Shirin na N-Power zai cigaba da kasancewa shirin samar da ayyukan yi na Renewed Hope a ƙarƙashin kulawar ministan agaji.

An Sallami Wasu Ƴan N-Power

A wani labarin kuma, kun ji cewa N-Power ta ce masu cin gajiyar shirin a zubin farko da na biyu (Batch A da B) ba sa cikin shirin a halin yanzu.

Sai dai, har yanzu masu kula da shirin a gwamnatin Tinubu sun yi shuru game da makomai wadanda aka dauka a karkashin zubi na uku da hudu (Batch C1 da C2).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng