Innalillahi: Matafiya 9 Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota
- An samu mummunan hatsarin mota a kan titin hanyar Ogbomosho zuwa Oyo wanda ya salwantar da rayukan mutum tara
- Hatsarin motan ya auku ne a tsakanin wata motar tirela da wata babbar mota a daren ranar Asabar
- Mutum tara daga cikin mutum 13 da hatsarin ya ritsa da su sun samu raunukan ƙuna daban-daban yayin da sauran suka tsira ba tare da rauni ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Matafiya tara cikin 13 sun samu raunukan ƙuna daban-daban a lokacin da motarsu ta yi karo da wata tirela a kan hanyar Ogbomoso zuwa Oyo a jihar Oyo a daren ranar Asabar, 2 ga watan Disamba.
Kwamandan hukumar FRSC reshen Oyo, Joshua Adekanye ya ce hatsarin da ya auku a ranar Asabar ya haɗa da wata tirela da wata babbar mota a unguwar Sekona da ke kan titin Ogbomoso zuwa Oyo, cewar rahoton PM News.
Adekanye ya ce tara daga cikin mutum 13 da hatsarin ya ritsa da su sun ƙone, yayin da wasu huɗu suka tsira da rayukansu babu raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hatsarin motan ya auku
"Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:30 na daren ranar Asabar, kuma babbbar motar ta kama da wuta yayin da tirelar ta yi karo da ita." A cewarsa.
"Ba za a iya gano ainihin musabbabin kama wa da wutar da babbar motar ta yi ba saboda ya auku ne da daddare."
Sai dai ya ce dalilin da ya sa tirelar ta yi karo da babbar motar na iya zama saboda yin gudun da wuce ƙima da wuce ta ba ta hanyar da ta dace ba.
A cewarsa, mutanen da suka ƙonen an kai su asibitin koyarwa na jami'ar Ilorin domin duba lafiyar su, inda ya ƙara da cewa jami'an hukumar na Ogbomoso da Oolo su ne suka gudanar da aikin ceton.
"Sauran hukumomin da suka gudanar da aukun ceton sun haɗa da hukumar kashe gobara da ƴan sanda na Odo-Oba." A cewarsa.
Adekanye ya yi kira ga masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiyen cikin dare, wucewar da ba ta dace ba da tuƙi mai hatsari domin tabbatar da kiyaye rayuka a kan hanya.
Rayukan Mutum 25 Sun Salwanta a. hatsarin Mota
A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutum 25 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Peke da ke kan titin Oko-Olowo- Bode-Saadu a ƙaramar hukumar Moro ta jihar Kwara.
Mutum 15 kuma sun samu raunuka daban-daban a gobarar da ta tashi bayan da wata tankar man fetur da wata babbar motar ɗaukar kaya suka yi karo.
Asali: Legit.ng