NDLEA Ta Kama Wata Mata, Bilkisu, a Hanyarta Na Zuwa Kai Wa 'Yan Bindiga Harsashi a Katsina

NDLEA Ta Kama Wata Mata, Bilkisu, a Hanyarta Na Zuwa Kai Wa 'Yan Bindiga Harsashi a Katsina

  • Jami'an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) sunyi nasarar kama wata mai kai wa yan bindiga harsashi a daji a hanyarta na zuwa Katsina don kai wa dan bindiga makamai
  • An kama Bilkisu Suleiman yar shekara 28 ne a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu yayin sintiri kan babban hanyar Zaria zuwa Kano da harsashi masu yawa a bakin leda cikin jakarta
  • Femi Babafemi, mai magana da yawun Hukumar NDLEA ya ce tuni dai an mika wacce ake zargin ga rundunar yan sandan jihar Kaduna domin zurfafa bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

FCT Abuja - Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ta ce ta kama wata mata yar shekara 28 mai suna Bilkisu Suleiman wacce ke kai wa yan bindiga harsashi.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani yayin da yan bindiga suka dawo titin Kaduna-Abuja, sun sace mutum 30

Direktan watsa labarai da wayar da kai, a hedkwatar NDLEA a Abuja, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 7 da watan Janairu.

An kama wata mata yar shekara 28 da ke kai wa yan bindiga harsashi a Katsina
NDLEA ta cafke wata Bilkisu Suleiman da ake zargi tana kai wa yan bindiga harsashi. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Bilkisu ne kan gaba cikin mutanen da ake zargi da NDLEA ta kama a sintirin da ta yi yayin bukukuwan sabuwar shekara a jihohin Kaduna, Legas, Niger, Kogi, Kano, Borno da Osun.

A ina aka kama Bilkisu?

Babafemi ya ce jami'an NDLEA sun kama Bilkisu ne a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu yayin sintiri kan babban hanyar Zaria zuwa Kano dauke da harsashi guda 249 masu tsawon 7.62mm boye cikin bakin leda a jakarta na hannu ta mata.

Wani sashi na sanarwa ya ce:

"Tana kan hanyar zuwa kauyen Kakumi ne a Jihar Katsina don kai wa wani dan bindigan da ba a riga an gano ko wanene ba harsashin yayin da aka kama ta.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta mayar ta Dayyabu mijin Hafsat gidan yari bisa zargin kashe Nafiu

"An kuma mika ta ga Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna domin su cigaba da bincike."

Jami'an Tsaro Sun Kama Mai Kai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri Da Abinci a Neja

A wani rahoton, Rundunar yan sanda a jihar Neja ta ce jami’anta da ke aiki a ofishin yankin Gawu-Babangida sun yi nasarar cafke wani matashi mai shekaru 24, Ibrahim Ali, da aka fi sani da Bajala da bisa zargin yana kai wa yan bindiga kayan abinci.

Kama Bajala na zuwa ne bayan cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne a Lambata a karamar hukumar Gurara a ranar 27 ga watan Janairu na 2023, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164