“Abun Dariya”: Kotu Ta Nemi Yaron da Aka Zarga da Satar Keke Ya Biya N2m Kudin Beli
- Wata kotun majistare da ke Ogba, Ikeja a jihar Lagas ta bayar da belin wani yaro da aka zarga da satar keke kan kudi naira miliyan 2
- Wani lauyan Najeriya, Olanipekun Tobi, ya koka a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Juma'a
- A cewar Olanipekun, irin wannan hukunci shine dalilin da yasa gidan yara halin Najeriya ya cika da jama'a
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ikeja, jihar Lagos - Wani lauyan Najeriya mai suna Olanipekun Tobi, ya koka bayan wata kotun majistare da ke Ogba, Ikeja a jihar Lagas ta bayar da belin wani yaro da aka zarga da satar keke kan kudi naira miliyan 2.
Olanipekun ya ce wannan ne dalilin da yasa gidan gyara hali ya cika da jama'a a Najeriya.
Ya kara da cewar farashin keken da aka zargi yaron da sacewa bai kai N50,000 ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @OlanipekunTobiD, a ranar Juma'a, 1 ga watan Disamba.
Ya rubuta:
"Akwai wata kotun majistare a Ogba, wacce ta kafa sharudan belin wani yaro da aka zarga da sace babur. Ku cinka sharudan?
"Naira miliyan 2!
"Belin naira miliyan boyu ga yaron da aka zarga da satar kek wanda bai ma kai ko 50k ba.
"Sannan kuna mamakin yadda aka yi kurkukunmu suka cika da mutane."
Yan Najeriya sun yi martani
Da yake martani ga sharadin belin alkalin kotun, fitaccen lauya, Inibehe Effiong, ya bayyana hakan a matsayin abin ban haushi da ban dariya!
Bani da katabus: Wanda ya kone takardar digirinsa ya yi bayanin dalilansa na bankawa takardunsa wuta
@InibeheEffiong:
"Abun ban haushi da dariya"
@Brown__Sophie:
"Abun haushi.
"Sannan za ku fada mani cewa alkalin kotun majistaren zai iya bacci da kyau da daddare."
@masurge7:
"Ina mamakin idan wadannan mutanen da ke kan benci mutane ne."
@EbunoluwaD_ :
"Wow
"Ta ina har suka zo da abubuwa irin wannan?
"Wannan wane irin abin ban dariya ne?"
Matashi ya yi girki mai tsada
A wani labari na daban, wani dan TikTok ya yi kokarin shirya abinci, amma sai ya kare da soya wayarsa kirar iPhone a maimakon haka. Ya yada yadda al'amarin ya faru a TikTok, inda abun ya yadu.
An san wayoyin iphone da shegen tsada, kama daga R6k zuwa sama da R30k, saboda haka kona daya an jikin tukunya ba karamin al'amari bane.
Asali: Legit.ng