Matashi Ya Nuna Yadda Wayar iPhone Dinsa Ta Makale a Tukunya Bayan Ya Yi Kuskure Wajen Girki

Matashi Ya Nuna Yadda Wayar iPhone Dinsa Ta Makale a Tukunya Bayan Ya Yi Kuskure Wajen Girki

  • Wani dan TikTok ya saura da konanniyar wayar iphone bayan ya yi kuskuren dafa ta a tukunya a maimakon abincinsa
  • Bidiyon da ya yadu ya nuno bakar wayar iPhone makale a karkashin tukunya, yayin da wasu mutane biyu suka yi kokarin cire ta da babban cokalin juya abinci
  • Masu kallo sun tausayawa mutum, amma sun cika da mamakin yadda ya iya yin irin wannan kuskure na ganganci

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Sam girki mai kamanci wasu mutane ba domin dai basu san yaya ake yinsa ba.

Wani dan TikTok ya yi kokarin shirya abinci, amma sai ya kare da soya wayarsa kirar iPhone a maimakon haka. Ya yada yadda al'amarin ya faru a TikTok, inda abun ya yadu.

Kara karanta wannan

Yadda yaran turawa da mahaifinsu suka sharbi kuka a filin jirgi kan rabuwa da mai aikinsu

Matashi ya soya waya
Matashi Ya Nuna Yadda Wayar iPhone Dinsa Ta Makale a Tukunya Bayan Ya Yi Kuskure Wajen Girki Hoto: Getty Images/TikTok/dlamott
Asali: UGC

An san wayoyin iphone da shegen tsada, kama daga R6k zuwa sama da R30k, saboda haka kona daya an jikin tukunya ba karamin al'amari bane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yaya ya soya iPhone dinsa?

Dan TikTok din mai suna @dlamott, ya wallafa wani bidiyo yana mai nuna konanniyar iPhone din makale a kasan tukunya.

Ya yi ba'a cewa wannan alamu ne daga sama cewa kada ya sake girka abinci a rayuwarsa. Ga dukkan alamu, ya bar wayar tasa ne a kan dakali sannan ya daura tukunyar mai zafi a kanta ba tare da ankara ba. Sakamkon haka sai ya narkar da roba da ita inda ya bata waya da tukunyarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Gabe ya yi martani:

"Ka yi kokarin girki ne?? KAN WAYARKA??!"

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya raba daloli a unguwa, Kirkinsa ya tsorata mata, sun tsere a bidiyo

Bkiesh:

"Shin wannan wayar iPhone 15 ce?? Cewa yanzu kana iya girki a kanta."

Dakota:

"Wannan na daya daga cikin dalilai da dama da yasa ba'a barin waya a kicin. Idan kana yi a gida ka nisance ta da risho da wajen wanke hannu."

Ashweena :

"A wannan gabar tukunyar kawai za ka tsira da ita."

evetanya1:

"Ya kamata ka bude gidan abinci."

Mai aiki ta sa turawa kuka

A wani labari na daban, wani bidiyo da ya yadu da yaran turawa suna sharban kuka a filin jirgin sama yayin da mai aikinsu zata tafi ya tsuma zukata a soshiyal midiya.

Mai aikin wacce ta kasance bakar fata da aka ambata da suna Rosie, ta rigada ta yi nisa lokacin da yaran wanda ya dauketa aiki suna ruga wajenta, inda suka ki bari ta tafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng