Yar Tsohon Shugaban Kasa Ta Zargi Iyaye da Lalata ’Ya’yansu da Shaye-Shaye, Ta Fadi Dalili

Yar Tsohon Shugaban Kasa Ta Zargi Iyaye da Lalata ’Ya’yansu da Shaye-Shaye, Ta Fadi Dalili

  • Aisha Babangida, ‘yar tsohon shugaban kasar Najeriya, Ibrahim Babangida, ta nuna damuwa kan yadda iyaye su ka yi sakaci a tarbiyan ‘ya’yansu
  • Aisha ta bayyana haka ne yayin wani babban taron Al-Habibiyya karo na 11 da aka gudanar a yau Asabar 2 ga watan Disamba
  • Ta ce abin takaici ne yadda iyaye ke shaye-shaye da kuma dura wa ‘ya’yansu don kada su dame su yayin da su ke neman hutawa

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Diyar tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, Aisha Babangida ta zargi iyaye da laifi kan shaye-shaye.

Aisha ta yi wannan zargin ne inda ta bukaci iyaye su zage dantse don ganin sun taimaka wurin rage yawan shaye-shaye a tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

'Yar tsohon shugaban kasa ta yi martani kan yadda iyaye ke sakaci da 'ya'yansu
Aisha Babangida ta roki iyaye da su kula da 'ya'yansu. Hoto: Aisha Babangida.
Asali: Facebook

Mene Aisha ke cewa kan shaye-shaye?

Har ila yau, babban limamin Al-Habibiyya, Sheikh Fuad Adeyemi da kuma hukumar NDLEA sun nemi hadin kan iyaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aisha ta yi wannan kiran ne yayin babban taron Al-Habibiya karo na goma 11 a yau Asabar 2 ga watan Disamba a Abuja, cewar Daily Trust.

Diyar tsohon shugaban kasar wacce ita ce shugabar Inganta Rayuwar Mata a Nahiyar Afirka ta ce na daga cikin gazawar iyaye wurin bata tarbiyan yara.

Ta ce mafi yawan iyaye sun gaza bai wa ‘ya’yansu tarbiyyar addinin Musulunci wanda ya kara yawan shaye-shaye.

Wane shawara Aisha ta bai wa iyaye kan shaye-shaye?

Ta ce:

“Tarbiya ta na farawa ne daga gida, mun samu labarin yadda wasu iyaye ke shan kwalaben shaye-shaye.
“Iyayen kuma su na koyawa yaransu wannan mummunar dabi’a saboda kada su dame su.”

Kara karanta wannan

Jerin manyan yan siyasar Najeriya 10 da aka haifa a watar Disamba

Aisha ta kara da cewa ya kamata a kara kaimi wurin wayar da kan jama’a don dakile wannan matsalar.

NDLEA ta kama makafi da safarar kwayoyi

A wani labarin, Hukumar NDLEA ta cafke wasu makafi har guda uku da su ke safarar miyagun kwayoyi a Kano.

An kama makafin ne bayan samun bayanan sirri inda ake zarginsu da safarar kwayoyin daga Legas zuwa Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.