An Yi Asarar Dukiya Sakamakon Gobara a Masallaci da Shaguna a Jigawa
- Gobara ta tashi a Karamar Hukumar Hadejia da ke jihar Jigawa inda ta lalata shaguna uku da wani sashi na masallaci
- Mai magana da yawun Hukumar Tsaro a NSCDC na Jigawa, Adamu Shehu ya tabbatar da afkuwar gobarar a ranar Asabar
- Shehu ya ce kawo yanzu ba a san ainihin sanadin gobarar ba amma an yi nasarar kashe wutan kuma ba a rasa rai ba
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Jihar Jigawa - Shaguna da kayayyaki masu daraja da kudinsa ya kai miliyoyi sun lalace a Bakin Kasuwa da ke Karamar Hukumar Hadejia na jihar Jigawa a ranar Juma'a.
Adamu Shehu, mai magana da yawun Hukumar Tsaro na NSCDC na jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu ya ce gobarar ta kone shaguna uku, rumfa da wani sashi na masallaci a unguwar, The Cable ta rahoto.
Ya ce:
"A ranar Juma'a misalin karfe 10.30 na dare, ofishin NSCDC na Hadejia ta samu kirar neman dauki game da gobara a rukunin shagunan da ke Bakin Kasuwa, Babban Kasuwan Hadejia.
"An tura tawagar masu yaki da ibtila'i zuwa wurin don kashe gobarar da ceto abubuwan da wutan bai kama ba da hana sata.
"Abin bakin ciki, a lokacin da suka isa, wutar ta riga ta cinya shagunan kayan waya uku, rumfa da wani sashi na masallaci."
Menene sanadin tashin gobarar?
Shehu ya yi bayanin cewa kawo yanzu ba a san abin da ya haifar da wutan ba.
Ya ce wani shaidan gani da ido, ya ce wutar ta tashi ne daga tartatsin wuta daga 'pole wire' da ke daya cikin shagunan, rahoton Daily Trust.
Shehu ya ce jami'an NSCDC, Hukumar Kashe Gobara da mazauna yankin suka kashe gobarar.
Ya kara da cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon wutan.
Asali: Legit.ng