“Ina Son Mahaifinsa Idan Yana Raye Don Allah”: Matashiya Ta Fadi Dalilinta Na Auren Tsoho
- Wata yar Najeriya da ta bayyana dalilin da yasa ta zabi auren tsoho ta ja hankalin jama'a a dandalin TikTok
- Matashiyar ta tuno da yadda take aiki a matsayin mai karbar baki a lokacin da ta ci karo da dattijon da ya canza rayuwarta
- Mutumin ya sanya ta makarantar girke-girke, ya siya mata shago, sannan ya kula da ita gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Bidiyon wata matashiya yar Najeriya wacce ta bayyana dalilinta na auren tsoho ya ja hankalin jama'a a TikTok.
Matashiyar ta tuna cewa tana aiki ne a matsayin mai karbar baki lokacin da ta hadu da dattijon wanda ya sauya rayuwarta.

Asali: TikTok
Mutumin ya sanya ta makarantar koyon girke-girke, ya sama mata shago, sannan ya fara kula da ita har zuwa lokacin da ya nemi aurenta.

Kara karanta wannan
Wata uwa mai 'ya'ya 22 da ke son karin yara 105 ta ba da labarinta yayin da aka kama mijinta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lokacin da ta aure shi, sai ya mayar da ita kasar Kanada, inda take rayuwa a yanzu, sannan a nan ne ta dauki bidiyo tana mai bayyana dalilinta na auren tsoho.
Jama'a sun yi martani
Olivia ta yi martani:
"Nuna mana mijinki."
Helen ta ce:
"Tsohon da nake matakin magana da shi a yanzu, yana so ya kasheni da shawarwari da dogon zance. Bari na gaggauta tura mai abun da sauran mutane ke yi."
Urboyfriend's bestie ta rubuta:
"Mijinki na da yaya da ya fi shi tsufa kuma ki ji dadin rayuwarki."
Daniel Tracy2 ta yi martani:
"Ina bukatar mahaifinsa don Allah."
LabankSgold ta yi martani:
"Babu mai bin ki bashi ki ji dadin rayuwarki."
Anastasia:
"Yar'uwa kada ki kula su. Tsoffin maza sun fi idab kika hadu da na kirki na yi daya a baya kuma ya fi sauran dadin sha'ani."

Kara karanta wannan
Dan Najeriya ya raba daloli a unguwa, Kirkinsa ya tsorata mata, sun tsere a bidiyo
Ayi Daniel:
"Ki ji dadin rayuwarki sannan ki gabatar da mu ga abokan mijinki."
Saurayi ya tarwatsa auren budurwarsa
A wani labari na daban, mun ji cewa an gano wata kyakkyawar amarya tana sharban kuka babu kakkautawa a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya.
Mutane sun taru a kanta, suna kokarin rarrashinta, amma sam ta kasa jin rarrashi yayin da ta ci gaba da kuka babu kakkautawa.
Asali: Legit.ng