“Na Fasa Asusun Alawus Dina”’: Yar Bautar Kasa Ta Cika da Murna Yayin da Ta Baje Kudin da Ta Tara
- Wata matashiyar budurwa da ke zaune a garin Benin ta baje kolin abun da ta iya tarawa bayan ta fasa asusun ajiye alawus dinta
- Yar bautar kasar ta ce tana ta tara kudin alawus da ake biyanta na bautar kasa tun 2022
- Matashiyar ta yi karin haske kan yadda ta cimma wannan nasara nata yayin da ta karfafawa sauran yan bautar kasa gwiwa kan bukatar tara kudi
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wata mai yi wa kasa hidima wacce ta shafe tsawon watanni 12 tana tara kudin alawus dinta ta baje kolin abun da ta samu bayan ta fasa asusunta na katako.
A cewar matashiyar mazauniyar Benin, tana siyar da asusun ajiyar kudi don haka ta yanke shawarar yi wa kanta amfani da daya.
Ta nuna tsantsar farin ciki kan yawan kudin da ta gani sannan ta nuna yadda ta kirga shi da taimakon mutanen da ta ambata a matsayin ' mambobin kwamiti'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da take wallafa bidiyon a TikTok, matashiyar ta bayyana cewa akwai bukatar mutum ya horar da kansa domin ya iya ajiye kudi. Ta rubuta:
"A matsayin dan bautar kasa kana iya ajiye kudi daga alawus dinka idan har zai iya horar da kanka fa, na fasa asusun alawus dina a yau sannan na cika da farin ciki idan kana bukatar asusun tara kudi ka ajiye sako a sashin sharhi sannan idan kana son sanin yadda na iya yin nawa ka tambayeni hankali kwance zan kuma yi bayanin irin wahalar da na sha yi wa kasata ta gado hidima."
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani ga bidiyonta
Adeogun Adebisi Temitope ta ce:
"Ina bukatar wannan don Allah."
Gandhibhoy ya ce:
"Yar'uwa na ajiye lambar asususna."
Jennyvee20 ta ce:
"Alawus dina ne ya cece ni."
An sako yar bautar kasa da aka sace
A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima ta ƙasa (NYSC) ta ce ta samu nasarar ceto ɗaya daga cikin ƴan mata bakwai da aka yi garkuwa da su a Zamfara.
Kakakin hukumar ta NYSC, Eddy Megwa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba, cewar rahoton The Punch.
Asali: Legit.ng