Dan Shekara 18 Ya Fadi Yadda Ya Kashe Tsohuwar Shugabar Makaranta Bayan Sace Wayarta a Ondo

Dan Shekara 18 Ya Fadi Yadda Ya Kashe Tsohuwar Shugabar Makaranta Bayan Sace Wayarta a Ondo

  • Wani karamin yaro, Mubarak Akadiri, ya bayyana yadda ya kashe tsohuwar shugabar makaranta bayan sace wayarta
  • Mubarak ya ce ya kashe dattijuwar ne wacce mahaifiyarsa ke yi wa aikin gyara gida ta hanyar rotsa ta da tabarya
  • Ya shaidawa kotu cewa marigayiyar ta ganshi lokacin da ya ke satar wayarta inda ta yi kokarin hana shi guduwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Akure, Ondo state - Wani yaro dan shekara 18 Mubarak Akadiri, ya bayyana yadda ya kashe tsohuwar shugabar makaranta, Misis Sidikat Adamolekun, bayan sace wayarta mai darajar naira dubu 66 a jihar Ondo.

Mahaifiyar yaron na aiki ne a gidan matar da yaron ya kashe, mai shekaru 62, kamar yadda Legit ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kamar almara: Matar aure ta datse igiyar aurenta na wata 6, bidiyon ya jawo muhawara

Dan shekara 18 ya kashe tsohuwar malamar makaranta a Ondo
Wani karamin yaro ya amsa laifin kashe tsohuwar malamar makaranta a Ondo kan kama shi da ta yi yana satar wayarta. Hoto: High Court
Asali: UGC

Yadda yaron ya kashe tsohuwar malamar makarantar

Ya shaidawa kotun majistire da ke Akure cewa ya kashe matar ne ta hanyar buga mata teburin katako bayan ta kamashi yana satar wayarta, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kamar dai kullum, na je gidan na yi aiki na, daga baya kuma na koma don na sace wayarta kirar Samsung.
"Sai dai cikin rashin sa a matar ta kama shi bayan satar wayar. Hakan ya sa ta rike ni, a kokarin na tsere, na dauki teburin katako na buga mata a kai.
"Matar ta ci gaba da ihu tana neman taimako, wannan ya sa na ci gaba da dukanta ta ko ta ina har ta fadi ta mutu."

A cewar sa.

Hukuncin da kotu ta yanke

Mai shari'a Damilola Sekoni ta umurci a kai ajiyar Mubarak gidan gyaran hali na Olokuta har zuwa lokacin jin ta bakin daraktan jami'an masu shigar da kara.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan matar da ta lakadawa mijinta duka saboda yana hira da yan mata

Sekoni ta dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Maris, 2024.

Mazauna gari a Kaduna sun tsere yayin da sojoji suka bar garin

A wani labarin, mazauna garin Maganda da ke gundumar Magajin Gari ta III a Birnin Gwari, jihar Kaduna, sun tsere daga gidajensu bayan janye sojojin da aka girke a garin.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan garin sun tsere ne don tsoron farmakin 'yan bindiga wadanda ke addabar garin tsawon shekaru, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.