Ikon Allah: Yan Ta'adda Sun Mutu Yayin Da Bam Din Da Suka Dasa Ya Tashi Da Su a Jihar Borno
- Mayakan kungiyar ISWAP huɗu sun sheka lahira yayin da bam ɗin da suka dasa ya tashi da su a jihar Borno
- Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun ɗana bam ɗin a hanyar wucewar sojoji amma makircin ya ƙare a kansu ranar Laraba
- Zagazola Makama ya tattaro cewa duk da ragargazar da aka yi musu, a yanzu yan ta'addan na neman dawo da tashin bama-bamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - 'Yan ta'adda huɗu na ƙungiyar ISWAP sun mutu yayin da bam ɗin da suka dasa ya tashi da su a ƙauyen San San, karamar hukumar Mobbor ta jihar Borno.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa mugun nufin yan ta'addan ya koma kansu sa'ilin da suka dasa bam a hanyar wucewar dakarun sojin birged ta 5 ranar Laraba da ta wuce.
Bayanai sun nuna cewa bayan sun ɗana bam ɗin sai ya tashi da su, ya yi musu gunduwa-gunduwa a wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun tono wani bam na daban
Bayan haka kuma, sojojin rundunar MNJTF na sashi na 4 da aka tura garin Chetima Wongonu sun tono wani bam da ake zargin yan ta'adda suka dasa a kusa da kauyen Chetimari.
Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce yan ta'adda sun ƙara matsawa wajen amfani da ababen fashewa
A rahoton da ya wallafa a shafinsa na X, Makama ya ce:
"Gabanin faruwar lamarin, mayaƙan ISWAP sun buɗe wuta a Chetimari da daddare da nufin jawo hankalin dakarun sojoji saboda idan sun fito zasu taka bam ɗin."
"Duk da wannan makircin sojojin suka nuna turjiya kuma daga bisani suka gano abun fashewar da ƴan ta'addan suka dasa da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, suka warware shi."
Ya kuma tattaro cewa duk da yadda aka yi raga-raga da yan ta'adda tare da lalata musu kayan aiki da kashe wasu da dama, a yanzu suna neman komawa amfani da abubuwan fashewa.
Dubun masu garkuwa 8 ya cika a Kaduna
A wani rahoton na daban Yan sanda sun kama yan bindiga takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a sassa daban-daban na jihar Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna, Mansir Hassan, ya faɗi sunayen waɗanda aka kama.
Asali: Legit.ng