Magidanci Ya Maka Matarsa a Gaban Kotu Kan Aure Bisa Aure, Ya Nemi Wata Bukata 1

Magidanci Ya Maka Matarsa a Gaban Kotu Kan Aure Bisa Aure, Ya Nemi Wata Bukata 1

  • Wani magidanci ya maka matarsa ta aure a gaban kotun shari'ar musulunci da ke Kano kan zarginta da yin aure kan aure
  • Magidancin ya gaya wa kotu cewa sun yi aure da matarsa lokacin suna ƙasar Saudiyya amma daga baya matarsa ta auri wani daban bayan ta dawo Najeriya
  • Sai dai, matar mai suna Zulaiha Hussaini ta musanta cewa akwai igiyar aure a tsakaninta da mai shigar da ƙarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wani ɗan Najeriya mazaunin ƙasar Saudiyya, Yakubu Yunusa, wanda aka fi sani da Dogo Mai Nama, ya maka matarsa ​​Zulaiha Hussaini, a gaban kotun shari’ar Musulunci.

Yakubu ya kai ƙarar matar ta sa ne bisa zarginta da laifin auren wani mutum, inda ya roƙi kotun da ta raba auren da ta yi na baya-bayan nan, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa manoma a gonakinsu, sun yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Taraba

Magidanci ya maka matarsa a gaban kotu
Magidanci ya kai karar matarsa a gaban kotu kan zargin aure bisa aure Hoto: tribuneonline.ng
Asali: UGC

Yadda aka ɗaura musu aure

Da yake gabatar da ƙararsa a gaban kotu a filin hockey da ke Kano ta hannun lauyansa, Wada Bashir Isyaku, Mai Nama ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na haɗu da Zulaiha a ƙasar Saudiyya a shekarar 2019, bayan na bayyana niyyar aurenta, sai na tambaye ta ko zan iya turo ƴan uwana zuwa ga danginta a Najeriya domin neman izinin aurenta, amma ta gaya min cewa za ta fara tuntubar danginta."
"Bayan haka, a ranar Juma’a a shekarar 2019, ta shaida min cewa ta tuntuɓi waliyinta ɗaya tilo a Najeriya, wato kawunta, wanda ke zaune a Maiduguri. Ta ce kawun nata ya shaida mata cewa babu bukatar in aiko da waliyyi kan auren da za a yi washegari saboda rashin tsaro a Maiduguri. Ta ce kawun nata ya ce zai nemi abokinsa ya zama waliyyi na."

Kara karanta wannan

Juyin mulki a kasar Saliyo? Abin da muka sani yayin da gwamnati ta sanya dokar hana fita

"Washegari ta kira ta gaya min kawunta ya tuntuɓe ta cewa an ɗaura aure a wannan rana bayan Sallar Azahar kuma yanzu mun yi aure."
"Domin murnar hakan, na raba goro da alawa, na ba ta Riyal 1,000 a matsayin sadaki, sannan na yi liyafar ɗaurin aure a Saudiyya, bayan nan ta koma gidana da ke Saudiyya."
"Lokacin da take ɗauke da cikin wata takwas, ta roke ni da in bari ta dawo Najeriya ta haifi jaririn saboda tana son mahaifiyarta ta kula da ita. Na yarda kuma ta zauna tare da matata ta farko a gidana da ke Hotoro, Kano. Ta haifi ƴar mu Hajara a shekarar 2020."
“Na sha biya mata bukatunta, ciki har da siyan rago a duk lokacin babbar Sallah, ko da ta koma garinsu a shekarar 2022."
"Watarana a shekarar 2022, na kira lambarta sau da yawa amma ba ta ɗauka ba, sai kawai wani mutum ya kira ni washegari ya gargade ni kada na kiran matarsa ​​da daddare. A lokacin ne na gano ta auri wani Ibrahim a Katsina kwanaki biyar da suka wuce."

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya bayyana mutum 1 mai juya akalar gwamnatin Tinubu

"Ina rokon kotu da ta raba auren nan ta mayar min da matata da 'ƴata."

Me nene martanin wacce ake ƙara?

Sai dai Zulaiha, ta bakin lauyanta, Nura Aminu Hausa, ta musanta cewa ta taɓa yin aure da mai ƙarar ba. Lauyan ya ce ba ta taɓa samun juna biyu ba kuma ba ta da wani dangi a Maiduguri kamar yadda mai shigar da ƙara ya yi iƙirari.

Lokacin da alƙalin kotun ya tambaye shi ko yana da shaidu, mai shigar da karar ya amsa da “Eh.”

Mai shari'a Abdullahi Halliru, ya umurci mai ƙara da ya gabatar da shaidunsa a zaman kotun na gaba.

Kotu Ta Raba Auren Shekara Hudu

A wani labarin kuma, wata babbar kotun yanki da ke birnin tarayya Abuja, ta raba auren wasu ma'aurata biyu da suka kwashe shekara huɗu suna tare.

Kotun ta datse igiyar auren da ke tsakanin ma'auratan ne saboda matar ta bayyana cewa ta daina sha'awar zama da mijinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng