Yan Bindiga Sun Rutsa Wasu Manoma a gonakinsu, Sun Yi Ajalin Mutum Biyu a Jihar Taraba
- Wasu miyagun yan bindiga sun rutsa manoma biyu a gonakinsu, sun yi ajalinsu a jihar Taraba da safiyar ranar Talata
- Bayanai daga yankin sun nuna cewa lamrin ya ƙara jefa tsoro da tashin hankali a zuƙatan mutane musamman mata da kananan yara
- Mai magana da yawun hukumar yan sandan Taraba ya ce suna ɗaukar matakan kakkabe dukkan yan bindiga daga jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kashe manoma biyu a gonakinsu a yankin Yangtu a jihar Taraba.
Kamar yadda Channels tv ta tattaro, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talara a kudancin jihar da ke shiyyar Arewa maso Gabas.
Tsohon ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ussa a majalisar dokokin Taraba, Habila Timothy, ya bayyana cewa manoman sun fito ne daga ƙauyen Kpambo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa manoman sun je gonarsu da ke Kwambai, garin da ya haɗa iyaka da ƙaramar hukumar da kuma yankin Yangtu.
Ya ce:
"Yanzu haka da nake magana da ku mutanen mu suna cikin ruɗani, sun rasa inda zasu sa kansu, mata da ƙananan yara suna ta kuka kuma nan ba da daɗewa ba dare zai shiga."
"Mutum nawa zan iya ɗauka zuwa wurare masu tsaro? Muna da tabbacin hanyar da zamu bi tana da tsaro? Muna matsanancin bukatar a kawo mana agaji domin zaman lafiya ya dawo."
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Amma a nasa ɓangaren, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya ce har yanzun rahoton bai kai ga ofishin ƴan sanda ba.
Ya kuma ƙara ba da tabbacin cewa hukumar ta ɗauki matakai kuma an yi nisa a kokarin kakkabe yan bindiga gaba ɗaya daga jihar, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Irin waɗan nan hare-hare ya tilastawa mafi yawan mazauna ƙauyukan yankin yin hijira zuwa wasu wuraren domin tsira da rayuwarsu.
An kashe jami'an tsaro a Anambra
A wani rahoton na daban Rayuka sun salwanta yayin da jami'an tsaro da yan bindiga suka yi artabu a jihar Anambra ranar Talata da safiya.
Rahoto ya nuna cewa musayar wutar ta ɗauki lokaci har sai da jami'an tsaron haɗin guiwa suka isa wurin, suka fatattaki yan ta'addan.
Asali: Legit.ng