Nasara Daga Allah: Hatsabiban 'Yan Bindiga Uku da Suka Addabi Mutane Sun Baƙunci Lahira
- Yan sanda da haɗin guiwar dakarun rundunar yan sa'kai sun halaka kasurguman yan bindiga uku a jihar Katsina
- Kwamishinan yan sandan jihar, Aliyu Abubakar Musa, ya ce an kashe yan ta'addan ne yayin sintirin jami'an tsaro a Jibia
- Ya kuma yi kira ga al'umma su ci gaba da taimakawa jami'ai da bayanan sirri domin kai ɗauki a lokacin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce dakarunta sun samu nasarar sheƙe manyan shugabannin ƴan bindiga uku a jihar.
Kwamishinan yan sandan jihar, CP Aliyu Abubakar Musa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar ranar Talata.
A rahoton Leadership, sanarwan ta ce dakarun ƴan sanda sun raba ƙasurguman yan bindigan da duniya yayin da suka fita sintiri tare da yan sa'kai na jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka yi musayar wuta
Kakakin yan sandan ya yi bayanin cewa yayin wannan sintiri, kwatsam ƴan bindigan suka buɗe wa tawagar jami'an tsaron wuta a yankin Kwarare, ƙaramar hukumar Jibia.
A cewarsa, nan take dakarun suka maida martani cikin kwarewa da sanin makamar aiki, wanda hakan ya tilastawa yan bindigan tserewa zuwa cikin daji.
A rahoton Daily Nigerian, mai magana da yawun yan sandan ya ce:
"Yayin da jami'an tsaron suka tsefe dajin gaba ɗaya, sun gano gawar yan ta'adda uku da suka baƙunci lahira da kuma babur guda ɗaya."
"Daga bisani an gano bayanan yan bindigan da aka kashe wanda suka haɗa da wani da ake kira Bala Wuta, ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi Jibia da kewaye."
"Sauran biyun sune, Dogo Na Sahara da Hassan Bukuru, a yanzu jami'ai sun ƙara matsa kaimi wajen bincike da nufin kamo waɗanda suka gudu."
Ya kuma ƙara da cewa kwamishinan ya roki dakarun kar su yi sanyi a yaƙin da suke da yan ta'adda har sai sun kakkabe su baki ɗaya.
Haka nan ya roki ɗaukacin mazauna jihar Katsina su ci gaba da taimakawa hukumomin tsaro da bayanan sirri domin ɗaukar matakin da ya dace.
Wasu mazauna karamar hukumar Ɗanja a Katsina, ɗaya daga cikin yankunan da lamarin yan bindiga ya shafa sun shaida wa Legit Hausa cewa an fara samun sauki.
Abdul Sabuwar Kasa, ya shaida wa wakilinmu cewa jami'an sa'kai da Gwamna Dikko Radda ya ɗauka aiki sun fara zakulo masu hannu musamman infoma.
"Gaskiya ana samun nasara a kansu, kwanan nan sauki na ƙara bayyana, yan bindiga biyu aka kashe a nan yankin mu, ɗaya imfoma ne, ɗaya kuma ɗan fulani ne dama an san shi."
"Muna fatan Allah ya sa wannan sauki ya ɗora ya zama silar samun zaman lafiya mai ɗorewa a Katsina da Najeriya baki ɗaya," in ji shi.
Malam Abdullahi, ya ce tabbatar da sha'anin tsaro ya fara gyaruwa a Katsina kuma suna fatan Allah ya ƙara taimakawa a matakan da gwamnati ke ɗauka.
Za a rataye wanda ya kashe maƙocinsa
A wani rahoton na daban Babbar kotun jiha ta ba da umarnin a rataye matashin da ya kashe maƙocinsa har lahira a jihar Ondo.
Yan sanda sun kama Joseph Abayomi, bisa zargin soka wa makoshinsa dan shekara 63 adda a Akure, babban birnin jihar.
Asali: Legit.ng