"Sun Ishe Ni da Hayaniya": Wani Mutum Ya Farmaki Coci da Karnukansa 3, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce
- An sha yar dirama da shiga rudu a lokacin wani shirin ibada a coci yayin da wani fusataccen mutum ya bayyana da karnuka guda uku
- Labarin ya nuna cewa hayaniyar yan cocin na damun makwabta kuma wannan ne yasa mutumin ya farmaki wajen bautan
- Mutane da dama da suka kalli bidiyon mutumin sun koka kan yadda cocina ke damun muhallinsu da hayaniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani dan gajeren bidiyo ya nuno lokacin da wani fusataccen mutum ya farmaki coci don nuna rashin jin dadinsa da yawan hayaniyarsu.
A cikin bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya, mutumin ya shiga harabar kotun tare da karnukansa guda uku yayin da ake tsaka da bauta.
Da alama zuwansa cocin ya kawo karan tsaye ga taron addu'o'i da suke yi inda masu bauta suka fuskance shi, yayin da wasu suke kallo cike da kosawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba a tabbatar da inda abun ya faru ba. Gist Ville wacce ta yada bidiyon mai dan dishi-dishi a Facebook ta yi masa take da "Wani mutum ya farmaki coci tare da karnukansa guda sannan ya yi kokarin hana su damun makwabta da hayaniyarsu.
Bidiyon ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.
Jama'a sun yi martani
Edeh Favour Ngozi ta ce:
"Akwai mutanen da ban haushi, suna damun suran jama'a da hayaniya, daga safe har zuwa dare, babu wanda ya damu da hargitsin da suke haddasawa. Ya yi masu kyau."
Chinyere Precious-emerald Okorie ta ce:
"Haba! Ya kamata cocina su dunga damuwa da makwabtansu. Hayaniyar da na'urorin ke haifarwa hankali baya iya duka."
"Suna iya rage karar zuwa kasa."
Esther Ijeoma ta ce:
"A inda nake zama, akwai cocina biyu suna kallon junansu.
"Ba ma bacci ko kadan duk dare hatta ga ranar Asabar. Eh, daya na yin taronta a yammacin Asabar yayin da dayar ke yin bitar wakoki."
Enare Ojong ya ce:
"Haka na kama wannan karamin yaron a masallaci wanda ke yi na sallar karfe 5:00 na asubahin nan."
Malamin addini ya caccaki masu wa'azi mata
A wani labarin, mun ji cewa Mike Bamiloye, wanda ya kafa cocin Mount Zion Faith Ministries, ya caccaki malaman addini mata wadanda ke yawon zuwa ko'ina amma suna bar wa yan uwa da masu aiki gidaje da mazajensu.
A wata wallafa da ya yi a Facebook a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, malamin kuma mai shirya fina-finai ya jaddada cewar malaman na yawon duniya, sannan suna wa'azi. Suna samun kulawa ta musamman yayin aikinsu na duniya amma sun bar mazajensu a gida su kadai.
Asali: Legit.ng