Gwamnatin Benue ta amince da sake bude wuraren bauta

Gwamnatin Benue ta amince da sake bude wuraren bauta

Gwamnatin jihar Benue ta amince da sake bude cocina da masallatai domin gudanar da harkokin bauta watanni biyu bayan rufewa sakamakon barkewar annobar Coronavirus.

Gwamnatin ta yi umurnin cewa ya zama dole a dunga bayar da tazara wajen bauta a cocina da masallatan.

Wannan shine shawarar da aka yanke a ranar Alhamis a Makurdi, a karshen wani taron hadin gwiwa na majalisar zartarwa ta jihar Benue da kwamitin yaki da COVID-19 a jihar karkashin jagorancin Gwamna Samuel Ortom.

Gwamnatin ta kuma yi umurnin bude kasuwanni sannan ta ce za a duba lamarin sake bude makarantu a kwanaki 14 masu zuwa.

Gwamnatin Benue ta amince da sake bude wuraren bauta
Gwamnatin Benue ta amince da sake bude wuraren bauta Hoto: Benue government
Asali: Facebook

Ta kuma umurci ma’aikata daga mataki na daya zuwa 12 wadanda aka bukaci su zauna gida kimanin watanni biyu da suka gabata da su koma bakin aiki, amma za su dunga sanya takunkumin fuska da bin dokar nesa-nesa yayinda za su aiki.

Da yake bayyana shawarar da aka yanke a karshen ganawar, Gwamna Samuel Ortom ya sanar da gyara a dokar kulle na safe zuwa dare da aka sanya a jihar kimanin watanni biyu da suka gabata.

A cewarsa, “an duba dokar kullen da aka sa a jihar, a yanzu zai kasance tsakanin karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe a kullun, har sai baba-ya-gani.

“Daga yau Alhamis, 21 ga watan Mayu, 2020, cocina da masallatai za su dunga gudanar da harkokin bauta.

“Hakan na nufin cewa cocina da masallatai da ke gudanar da taron addini sau biyu a baya na iya gudanarwa sau hudu a rana daga yanzu.

“An yarda da kasuwanci a unguwa amma a bi dokar nesa-nesa da juna. Za a bude kasuwanni domin ba yan kasuwa damar bude shagunansu yayinda za a dunga yiwa kasuwanni fashi lokaci zuwa lokaci.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Ba mu yi fushi ba, za mu sake tura tawagar kwararru Kogi - FG

“Har yanzu batun haramta tafiye-tafiye na nan, sai dai na abubuwan amfani. Ya karfafa wa mutanen Benue gwiwar jajircewa kan harkar noma yayinda ake fuskantar shiga koma bayan tattalin arziki,” in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel