Dalibar OAU Ta Tsinci Kanta a Asibiti Bayan Shafe Awa 58 Ta Na Wanki Babu Kakkautawa, Hannun Ya Jeme

Dalibar OAU Ta Tsinci Kanta a Asibiti Bayan Shafe Awa 58 Ta Na Wanki Babu Kakkautawa, Hannun Ya Jeme

  • Wata dalibar Jami'ar Obafemi Awolowo ta kafa tarihi yayin da ta kwashe awanni 58 ta na wanki a jihar Osun
  • Dalibar mai suna Subair Enitan ta fara wankin ne na awanni 50 don shiga kundin bajinta ta Guinness a rayuwarta
  • Sai dai a karshe ta tsinci kanta a asibiti bayan kammala wankin na awanni 58 saboda yadda hannayenta su ka jeme

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Dalibar Jami'ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun, Subair Enitan da ta ke kokarin kafa tarihi ta kare a asibiti.

Enitan ta fara wanki har na tsawon awanni 50 don shiga kundin bajinta na Guinness inda ta yi wankin har na tsawon awanni 58.

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake babbar kasuwar Kabba a jihar Kogi, an yi asarar dukiya ta miliyoyin naira

Daliba ta kwana a asibit bayan shafe awa 58 ta na wanki
Dalibar ta sha alwashin shafe awanni 50 ta na wanki. Hoto: @_Dr_Bush_.
Asali: Twitter

Mene ya faru da dalibar a karshe?

Sai dai kuma a karshe ta tsinci kanta a asibiti bayan hannayenta sun jeme saboda dadewar da ta yi ta na wankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Enitan ta fara wannan gasa ce a ranar Juma'a 24 ga watan Nuwamba don shiga tarihi a rayuwarta.

Dalibar ta fara wankin ne da misalin karfe 2:35 na rana a cikin harabar makarantar da ke jihar, cewar Vanguard.

Zuwa ranar Litinin 27 ga watan Nuwamba da misalin karfe 12:05 da dare Enitan ta kammala wankin inda ta zarta ainihin awannin da ta so yi.

A cikin wani faifan bidiyo da Punch ta yada an gano Enitan a kwance a gadon asibiti bayan cimma burinta.

Wane martani Enitan ta yi ga mutane?

Yayin da ta ke magana bayan kammala wankin Enita ta ce tun a baya ta so ta janye amma sai ta na jin kwarin gwiwar za ta iya yi.

Kara karanta wannan

Malaman makaranta ta fadi mataciyya a jihar Ogun, abokan aikinta sun bayyana dalilin mutuwarta

Ta godewa mahaifiyarta da ke wurin da kuma sauran kawayenta inda ta ce ta samu karfin gwiwa da zuwansu.

Har yanzu kundin bajinta na Guinness bai ce komai ba game da wannan bajinta ta dalibar.

Guinness ta lamuncewa matashi wakar awa 200

A wani labarin. kundin bajinta na Guinness ya lamuncewa dan Najeriya waka har ta tsawon awanni 200.

A ranar 10 ga watan Yuni, Oluwatobi ya wallafa a Instagram cewa Guinness ya amince da bukatarsa na shafe tsawon awanni 200 yana rera waka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.