Sarki Ya Raba Wa Mutanensa Tukunyar Girki Na Gas, Ya Yi Gargadi Su Daina Amfani da Itace

Sarki Ya Raba Wa Mutanensa Tukunyar Girki Na Gas, Ya Yi Gargadi Su Daina Amfani da Itace

  • Gidauniyar Oba Saheed Ademola Elegushi, ta hanyar shirinta na ‘shara domin gas’ na ɗorewar muhalli ta gudanar da shirin musanya a yankin Ikate
  • A cikin shirin, mazauna wurin sun musanya sharar su da tukunyar iskar gas, da manufar samar da makamashi mai tsafta
  • Wani rahoton kafofin watsa labarai ya ce Oba Elegushi ya hana yin amfani da itacen wuta domin dafa abinci tare da ƙarfafa gwiwar yin amfani da gas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Elegushi, jihar Legas - Kimanin iyalai 200 ne a yankin Ikate/Elegushi da ke jihar Legas suka ci gajiyar shirin ‘shara domin gas'.

Tsarin wani shiri ne na samun ɗorewar muhalli na gidauniyar Oba Saheed Elegushi.

Oba Elegushi ya raba tukunyar gas
Oba Elegushi ya raba wa mutanensa tukunyar iskar gas Hoto: Oba Saheed Ademola Elegushi, Lekan Bakare Foundation
Asali: Facebook

Mutane suna musanya shara da tukunyar gas

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Yan majalisa 27 cikin 31 sun juya wa gwamnan PDP baya yayin da ake yunkurin tsige shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) shirin ‘shara domin gas’ na haɗin gwiwa ne da kamfanin Smart Gas, kuma yana da burin kiyaye tsaftar muhalli.

Da yake jawabi ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin a ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba, babban jami’in gudanarwa na kamfanin Smart Gas, Yinka Opeke, ya ce sun gudanar da gangamin ne domin inganta amfani da iskar gas a madadin kalanzir da gawayi.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Oba Elegushi ya yi gargaɗi kan amfani da itacen wuta saboda yana hana rayuwa mai inganci.

Sarkin na Legas ya samu yabo saboda gudunmuwar da ya bayar wajen samar da shirin tsaftataccen muhalli.

Opeke ya bayyana cewa:

"Yin amfani da itacen wuta da gawayi wajen girki ba wai kawai yana illa ga muhallinmu ba saboda hayakin da ake fitarwa amma har da lafiyar ku saboda hayakin da mata da ƙananan yara ke shaƙa.

Kara karanta wannan

Bayan Uba Sani, Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci kan nasarar wani gwamnan APC

"Mun gabatar da wannan shirin ne ga Oba kuma ya ga ya dace ya kawo muku shi, shi ya sa a yau ya ba da kuɗin waɗannan tukunyar gas ɗin."
"Za mu musanya sharar ku da tukunyar gas ɗin mu, ta yadda za mu bar muku wata unguwa mai lafiya da tsafta."

A nasa jawabin, Muyiwa Gbadegesin, manajan darakta (MD) na hukumar kula da shara ta Jihar Legas (LAWMA), ya yaba da shirin, inda ya ce zai ceto muhalli.

Farashin Gas Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

A wani labarin kuma, farashin gas na girki ya yi tashin gwauron zabi inda ya kai N1,000 kan kowane kg.

Ƴan Najeriya da dama sun koka kan tashin gwauron da gas ɗin girki ya yi, a daidai lokacin da ake cikin halin matsi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng