Gobara Ta Babbake Babbar Kasuwar Kabba a Jihar Kogi, an Yi Asarar Dukiya Ta Miliyoyin Naira

Gobara Ta Babbake Babbar Kasuwar Kabba a Jihar Kogi, an Yi Asarar Dukiya Ta Miliyoyin Naira

  • Rahotanni sun nuna cewa goba ta tashi a babbar kasuwar Kabba da ke jihar Kogi, inda ta lakume shaguna masu tarin yawa
  • Kasuwar wacce ta tashi da karfe 5 na Asuba, an gaza kashe ta yayin da 'yan kasuwa ke kallon miliyoyin dukuyoyinsu na ci da wuta
  • Har yanzu ba a san musabbabin abin da ya jawo tashin gobarar ba, sai dai jami'ai na zargin wutar lantarki ce ta haddasa ta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kogi - Wata gobara da ta tashi a Asubahin ranar Litinin, ta jawo asarar miliyoyin naira a wani bangare na babbar kasuwar Kabba a jihar Kogi.

Gobarar ta lakume shaguna masu tarin yawa, yayin da ta bar 'yan kasuwa da mazauna yankin cikin tashin hankali, babu wanda ya iya shawo kanta.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa sun rike basaraken Abuja da yayansa 3, sun sako matarsa don nemo kudin fansa

Hukumar kashe gobara/Jihar Kogi/Kasuwar Kabba
Har yanzu ba a san musabbabin abin da ya jawo tashin gobarar ba, sai dai jami'ai na zargin wutar lantarki ce ta haddasa ta. Hoto: @Fedfireng
Asali: Twitter

Yunkurin kashe gobarar ya ci tura, yan kasuwa sun saduda

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5 na Asuba, inda ta mamaye kasuwar tare da cinye shaguna masu yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin jama'a na kai dauki don kashe gobarar tare da dakileta daga yaduwa ya ci tura, ana kashe ta kamar ana kara rura ta ne, ta gagari kowa.

Wani da abin ya faru gaban idonsa ya ce haka 'yan kasuwa suka saduda, suna kallo kayansu na ci da wuta amma babu wanda zai iya yin wani abu akai.

Ana zargin wutar lantarki ce ta haddasa gobarar

Kasuwar wacce ta yi shuhura wajen hada-hadar kayan gona, tufafi, kayayyakin wutar lantarki, kayan daki da sauransu, yanzu ta zama toka.

Har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar gobarar, yayin da jami'ai ke tunanin ko wutar lantarki ce ta jawo hakan.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna

A hannu daya, wani mazaunin Kabba ya ce rashin ababen kashe gobara a kasuwar ya taimaka wajen yaduwar gobarar, inda ya ce da an samu sauki idan akwai kayan.

Gobara ta tashi a babbar kasuwar sayar da kayan Samsung a Abuja

A wani labarin, wata mummunar gobara ta tashi a daya daga cikin manyan shagunan da ke sayar da kayan kamfanin Samsung a Abuja.

Babban shagon wanda ya ke a yankin Banex da ke gundumar Wuse 2, cikin kwaryar babban birnin tarayyar Najeriya, ya kama da wuta gadan-gadan ba tare da an iya shawo kanta ba, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.