Jami’an hukumar kashe gobara ta Kano ta tseratar da mutane 11 da dukiyar naira miliyan 33

Jami’an hukumar kashe gobara ta Kano ta tseratar da mutane 11 da dukiyar naira miliyan 33

Hukumar kashe gobara ta jahar Kano ta sanar da tseratar da mutane 11 daga mutuwa a cikin wasu gobara guda 97 da suka auku a cikin shekarar 2019, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai magana da yawun hukumar, Saidu Muhammad ne ya bayyana haka inda yace sun kubutar da mutane 11 da kadarori na naira miliyan 33 daga gobara 97 da suka faru a shekarar 2019 a Kano.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun kai ma jirgin Kaduna – Abuja hari

Malam Saidu ya bayyana ma menema labaru hakan ne a Kano a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu, inda yace mutane uku sun mutu a gobara a Kano a shekarar 2019, haka zalika an yi asarar dukiya da ta kai naira miliyan 15.

Ya kara da cewa a shekarar 2019, sun amsa kiraye kirayen mutane na hakikai sau 9, yayin da sun samu kiraye kirayen karya guda 10. Saidu ya bayyana sakaci wajen amfani da tukunyar girka ta iskar gas a matsayin babban abin da ya janyo gobara a Kano a shekarar 2019.

Sauran dalilan da suka haddasa gobara a jahar Kano sun hada da amfani da kayan wuta marasa inganci, amfani da na’urar dafa wuta ‘heater’, da kuma rashin iya janyo wuta zuwa cikin gida.

Daga karshe kaakaki Saidu ya yi kira ga jama’a da su guji amfani da kayan wuta ta hanyoyin da bai kamata ba, sa’annan ya shawarcesu dasu daina ajiye man fetir a gidajensu, musamman a lokacin hunturu don magance yiwuwar tashin gobara.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun bude ma jirgin kasa wuta a kan hanyarsa ta zuwa babban birnin tarayya Abuja daga jahar Kaduna.

Jirgin ya tashi daga tashar jirgin kasa dake garin Rigasa na jahar Kaduna da misalin karfe 10 na safe, sai dai bai yi nisa ba ya ci karo da yan bindiga a daidai garin Katari, kimanin kilomita 70 kafin shiga Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel