Matashi Dan Bauchi Ya Sauya Sunan ’Yarsa Zuwa Na Mahaifiyar Tinubu, Ya Bayyana Dalilin Hakan

Matashi Dan Bauchi Ya Sauya Sunan ’Yarsa Zuwa Na Mahaifiyar Tinubu, Ya Bayyana Dalilin Hakan

  • Matashi Khamees Darazo daga jihar Bauchi ya yi abin bajinta bayan sauya sunan 'yarsa zuwa na mahaifiyar Shugaba Tinubu, Abibatu
  • Khamees ya ce ya yi hakan ne ba don komai ba sai don kawai yadda ya ke tsananin son shugaban da kuma kudirorinsa
  • Matashin ya sauya sunan 'yar tasa mai shekaru biyu, Hauwa zuwa sunan mahaifiyar Shugaba Tinubu, Abibatu saboda kauna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Wani matashi a jihar Bauchi mai suna Khamees Darazo ya nuna irin kaunar da ya ke nuna wa Shugaba Bola Tinubu.

Matashin ya nuna hakan ne yayin da ya sauya sunan 'yarsa mai shekaru biyu zuwa sunan mahaifiyar Shugaba Tinubu, Abibatu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi bangare 1 tak da yafi bai wa muhimmanci a gwamnatinsa, ya ba da shawara

Matashi ya sauya sunan 'yarsa zuwa ga mahaifiyar Tinubu a Bauchi
Matashin ya cika alkawarin da ya yi wa Shugaba Tinubu. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wane suna matashin ya saka don Tinubu?

Khamees ya sauya sunan 'yar tasa mai suna Hauwa zuwa Abibatu a jiya Asabar 25 ga watan Nuwamba, Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darazo ya bayyana haka ne a walimar bikin sunan tare da abokansa a Bauchi inda ya ce ya yi haka ne saboda son da ya ke yi wa Tinubu.

Ya ce:

"Farkon nuna kaunata ga Tinubu shi ne lokacin da na sadaukar da alawus dina na bautar kasa lokacin da na ke bautar kasa a Gombe.
"Na yi hakan ne don kara masa karfi yayin da ake ci gaba da kamfe na yakin neman zaben 2023."

Don mene matashin ya yi haka ga Tinubu?

Ya ce ya yi hakan ne ba wai don neman wani abu ba sai dai don irin son da ya ke yi wa Tinubu inda ya ce shi babban dan kasuwa ne, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi gwaggwabar kyauta ga wadanda su ka lashe musabaka, Bala Lau ya yi martani

Ya kara da cewa:

"Na sauya sunan 'yata, Hauwa zuwa Abibatu wacce ita ce mahaifiyar Shugaba Tinubu.
"Na yi hakan ne don kara gode mata da irin kokarin da ta yi na tarbiyantar da shugaban kasa, Bola Tinubu a matsayin shugaba."

Matashi ya yi alkawarin saka sunan mahaifiyar Tinubu

A wani labarin, Matashi mai suna Khamees Darazo a jihar Bauchi ya sha alwashin sauya sunan 'yarsa zuwa ga mahaifiyar Tinubu.

Matashin wanda shi ne shugaban wayar da kan matasan Arewa ya bayyana haka a ranar 21 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.