Malaman Makaranta Ta Fadi Mataciyya a Jihar Ogun, Abokan Aikinta Sun Bayyana Dalilin Mutuwarta
- Misis Oluwatosin Aina, wata malamar makaranta a Ijebu Igbo, Jihar Ogun, an rahoto ta fadi mataciyya a Olokinne High School, inda ta ke aiki
- Marigayiyar ta dauki izinin ta tafi asibiti a lokacin da ta ke jin bata jin dadin jikinta amma ta rasu bayan dan lokaci
- Lamarin ya nuna korafin da aka yi dangane da tasirin da karancin malamai da tsananin damuwa ke yi kan lafiyarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ijebu Igbo, Jihar Ogun - Wata malama yar Najeriya da ke aiki a Olokinne High School, Ijebu Igbo a karamar hukumar Ijebu North na jihar Ogun, Misis Oluwatosin Aina, ta riga mu gidan gaskiya.
Misis Aina, wacce aka ce ta haura shekaru 50, ta fadi ne a makaranta ta kuma rasu jim kadan bayan samun izini ta tafi asibiti lokacin da ta fara yin rashin lafiya a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba.
An rahoto cewa an garzaya da ita wani sashi na Asibitin Koyarwa na Jami'ar Olabisi Onabanjo, Ijebu Igbo na jihar, inda likita ya tabbatar ta rasu, The Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayiyar, a cewar Vanguard, malama ce da ka mataki na 14 kuma tana koyar da Darrusan Addinin Kirista ne.
A nakalto wata majiya na cewa:
"Na ji cewa ba ta jin dadi bayan ta iso makaranta kuma ta samu izini daga shugaban makarantan domin ta tafi asibiti ta nemi magani amma ta fadi a kusa da motarta.
"An tabbatar ta rasu lokacin da aka garzaya da ita asibiti."
Ana zargin malamai na mutuwa saboda tsananin damuwa
Da ya ke magana a kan abin bakin cikin, wani malami da ke aiki a yankin ya nuna damuwa kan yadda malamai ke yawan mutuwa a jihar.
Malamin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce tsananin damuwa da samun karancin malamai na shafar lafiyar kalilan malaman da ke koyarwa.
Shugaban kungiyar malamai ya yi magana
Kazalika, shugaban malamai masu koyarwa a makarantun sakandare, na jihar Ogun, Felix Ogunsanwa, ya jajantawa iyalan malaman da ta rasu.
Agbesanwa shima ya tabbatar da cewa kungiyar ta san kallubalen karancin malamai da ke koyarwa a makarantu.
Duk da haka, ya ce gwamnatin jihar Ogun a baya-bayan nan ta bai wa malamai na wucin gadi na OgunTeach su 1000 takardan kama aiki na dindindin.
Agbesanwa ya mika godiya bisa kokarin gwamnatin ya kuma yi kira ga Gwamna Dapo Abiodun ya warware sauran matsaloli zai taimakawa malamai samun walwala kamar yadda ya yi alkawari.
Asali: Legit.ng