Malamin Addini Ya Dira Kan Mata Da Ke Hana Mazajensu Hakkin Kwanciyar Aure, Ya Fadi Halayensu
- Fasto Mike Bamiloye ya yi kakkausar suka ga mata masu hana mazajensu kusantarsu a yayin kwanciya
- Fasto ya ce akwai wasu mata musamman Kiristoci da ke zuwa coci su nuna su na Allah ne amma a cikin gidajensu ba su da dadi
- Ya ce irin wadannan mata ba su da mutunci kuma sun raina mazajensu sannan sun kasance marowata wurin ba da jikinsu
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shahararren Fasto a Najeriya, Mike Bamiloye ya caccaki mata musamman Kiristoci da ke hana mazajensu jin dadin kwanciyar aure.
Bamiloye wanda shi ne shugaban cocin Mount Zion Faith ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a yau Asabar 25 ga watan Nuwamba.
Wane hali matan ke nunawa a coci?
Mike ya ce mafi yawan wadannan mata su na nuna su na kirki ne a coci amma a gidajensu sun zama shaidanu, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce duk matar da ta ke haka ta cika butulu mai rashin mutunci da kuma kasancewa marowaciyar jikinta ga mijinta.
Ya ce:
"Wasu matan auren su na aikata abin da su ke so a gidajen aurensu, ba sa yi wa mazajensu biyayya."
Wane addu'a Faston ya yi wa matan?
"A coci za ka gansu kullum kusa da mazajensu su na dariya amma a gida ba haka halayensu ya ke ba.
"Irin wadannan mata a gidajensu ba su da mutunci kuma sun raina mazajensu, sannan sun zama marowata yayin ba da jikinsu ga mazajensu."
Faston ya kara da cewa irin wadannan sai yadda su ka ga dama su ke yi da jikinsu, ba su da dadi a gida amma a coci kuma kullum su na nuna sun fi kusa da ubangiji, mu na fatan ya shirye su.
Faston ya ce an takura shi da neman takara
A wani labarin, Shahararren Fasto a Arewacin Najeriya, Mathew Hassan Kukah ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke yawan damunshi kan neman shugabancin kasar.
Kukah ya ce akalla ya shafe shekaru 30 ya na fama da mutane da ke cewa har fom na takara za su siya mishi.
Sai dai Fasto ya ce shi kwata-kwata ba ya bukata kuma ya sani ba zai zama shugaba mai kyau ba.
Asali: Legit.ng