Kaciyar Mata: Gwamnan PDP Ya Haramta Al’adar a Fadin Jiharsa, an Bayyana Illarta Ga Mata
- Jihar Osun ta haramta kaciyar mata a gaba daya fadin jihar inda ta gargadi masu aikata hakan da su guji fushin hukuma
- Gamayyar jami’an tsaro daga bangarori da dama a jihar sun sha alwashin hukunta duk wani wanda aka samu da aikata laifin
- Wannan mataki na zuwa ne biyo bayan hadin gwiwa da ma’aikatun lafiya da na mata a jihar su ka yi kan matsalar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun – Hukumomi a jihar Osun sun sha alwashin hukunta duk wadanda ke yi wa mata kaciya a kokarin dakile al’adar a jihar.
Gamayyar jami’an tsaron ‘yan sanda da hukumar NSCDC da sauran ‘yan sa kai ne su ka bayyana haka a karamar hukumar Ilesa ta Gabas.
Wane mataki aka dauka kan kaciyar mata?
Taron wanda cibiyar Action Health Incorporated ta jagoranta ta bayyana himmatuwarta wurin aiki da masu ruwa da tsaki wurin dakile al’adar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mataki ya biyo bayan hadin gwiwa da ma’aikatun lafiya da na mata a jihar su ka yi kan wannan matsalar, Daily Trust ta tattaro.
Wakili daga ma’aikatar lafiya a jihar, Toyin Adelowokan ta bayyana cewa kaciyar mata ba ta da wani amfani ga lafiya sannan kuma barazana ce ga mata.
Shin kaciyar mata ya sabawa dokar kasa?
Toyin ta ce yi wa mata kaciya ya saba dokokin kasa kuma duk wanda aka cafke da aikata haka zai fuskanci hukunci, The Guardian News ta tattaro.
Jami’ar cibiyar AHI, Fatima Idris ta bukaci jami’an tsaro da su tabbatar sun kare martabar wadanda su ka kawo rahoton masu kaciyar mata ofishinsu.
Cibiyar ta bayyana cewa kaciyar ba ta da wani fa'ida sai dai jawo matsaloli munana ga rayuwar mata.
‘Yan sanda sun cafke dan takarar gwamnan kan damfara
A wani labarin, rundunar ‘yan sanda ta cafke wani dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP a jihar Kuros Riba kan zargin damfara.
Wanda ake zargin mai suna Wilfred Bonse ya damfari kamfanin Patricia kimanin naira miliyan 607.
Rundunar ‘yan sandan ta ce Wilfred ya dade ya na damfarar kamfanin inda ya ke hada baki da wasu masu damfarar yanar gizo.
Asali: Legit.ng