Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Matarsa Sun Yi Bikin Cika Shekaru 34 da Aure

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Matarsa Sun Yi Bikin Cika Shekaru 34 da Aure

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo da matarsa suna bikin cika shekaru 34 da aure
  • Domin tunawa da inda suka kai a rayuwa, Osinbajo ya wallafa wasu bidiyo da hotuna masu kayatarwa don godewa matarsa da nuna soyayyarsa a gareta
  • Osinbajo ya tunatar da duniya muhimmanci da matsayin kyakkyawar matarsa yayin da ya bata tabbacin samun karin shekaru masu inganci a gaba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo da matarsa, Dolapo, suna murnar cika shekaru 34 da aure.

Farfesa Osinbajo ya wallafa wani bidiyo a Instagram a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, inda ya kokawa matarsa cewa ya fara rasa karfinsa.

Osinbajo da matarsa sun cika shekaru 34 da aure
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Matarsa Sun Yi Bikin Cika Shekaru 34 da Aure Hoto: @profosibanjo
Asali: Instagram

A wasu jerin hotuna kuma, an gano shi sanye da wasu takalma dauke da taken "Dolly", sunan da ake kiran matarsa da shi rubuce a kansu; yayin da matar kuma ta sanya wanda aka rubuta "Prof".

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga tsakani yayin da yan majalisa suka fara shirin tsige gwamnan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A taken wallafarsa, Osinbajo ya taya matarsa murnar zagayowar ranar aurensu yayin da suka murnar shafe shekaru da dama tare a matsayin mata da miji.

"Zuwa ga Dolly,
"Aba ta mai kyau da ni'ima ta musamman daga wurin Ubangiji: yau mun shafe shekaru 34 masu ban mamaki, ina tayaki murnar zagayowar wannan rana @dolapoosinbajo !!!!"

Ga wallafarsa a kasa:

Jama'a sun taya Osinajo murna

balo_ng:

"Matarka masoyiyarka macece mai hankali. Kun yi kyau da juna, daya daga cikin ma'aurata mafi kyawu da za ka gani ko'ina a duniya. Karin shekaru masu yawa a tare."

flakes_ff:

"Awwww ban taba ganin wannan bangare naka na raha ba yallabai, shakuwarku mai ban mamaki abun son kallo ne ga kowa. Ya Ubangiji ka ci gaba da kebance wannan shakuwa cikin soyayyarka. Na taya ku murnar zagowar wannan rana Yallabai da yallabiya."

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

vanessa_kelechi:

"Barka da zagayowar wannan rana: Allah ya sa labarin aurenku ya ci gaba da karfafawa mutane masu gaskiya gwiwa don samun gidan aure na Allah. Allah ya lullube gidanku.

Duk namijin da ya sameni ya caba, Budurwa

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa wacce ke da hannu daya ta yada wani bidiyo a TikTok inda ta ce komai ya ji a jikinta.

A cikin bidiyon, matashiyar mai suna Maryann Officiall, ta zage tana kwasar rawa a cikin wani daki tana mai baje kolin dirarren surar jikinta mai matukar kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng