Babban Malamin Addini Ya Bayyana Mutum 1 Mai Juya Akalar Gwamnatin Tinubu
- An rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya a watan Mayu, watanni biyu bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2023
- Ana dai kallon Tinubu a matsayin wanda ya dade yana rike da madafun iko a ƙasar nan, mtarsa Oluremi ta kasance a cikin mulki tun 1999
- Wani malamin addini Fasto Ayuba Azzaman, ya yi magana kan rawar da ake zargin Oluremi tana taka wa a wannan gwamnatin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Kaduna, jihar Kaduna - Babban Fasto na cocin King Worship Chapel and Ministry, David Ayuba Azzaman ya ce Oluremi Tinubu, uwargidan shugaban ƙasa, "ita ce ke juya akala" a gwamnatin nan mai ci.
Fasto Azzaman wanda ya bayyana hakan kwanan nan ta shafinsa na Facebook, ya kuma bayyana cewa Oluremi Tinubu “tana goyon bayan mijinta”, Bola Ahmed.
Remi Tinubu tana goyon mijinta: Azzaman
Malamin addinin ya yi iƙirarin cewa a kusa da watan Yuli 2023, ya samu "wahayi" inda ya lura da Oluremi "a tsakiyar" wani gagarumin aiki a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɓangare na rubutun Azzaman yana cewa:
"Kusan wata ɗaya da ya wuce a cikin dare, na ga mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da matarsa Fasto Oluremi Tinubu, da wasu gungun mutane tare da su."
"Na lura Fasto Remi Tinubu tana tsakiya yayin da mijin na gefenta. Ita ce a tsakiyar wasu ayyukan da ke gudana, hankalin mutane ya fi karkata a a kanta fiye da maigidanta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu."
"Ko kun yarda ko ba ku yarda ba Fasto Remi Tinubu ita ce juya akalar wannan gwamnatin tana goyon bayan mijinta.”
Shugaba Tinubu Ya Shawarci Gwamnoni
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da wasu gwamnoni biyu na jihohin Kogi da Imo, tare da zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo.
Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnonin da su riƙa sanya maslahar al’umma a gaba, su yi aiki tukuru domin inganta jihohinsu.
Asali: Legit.ng