Mufti Menk ya kai ziyara fadar Tinubu, ya ce Najeriya za ta iya zama kasa mafi bunkasa a Afirka
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tarbi babban bako a fadarsa da ke babban birnin tarayya Abuja
- Fitaccen malamin Musulunci, Mufti Menk ya ziyarci fadar Tinubu a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba
- Mufti ya yi jawabi kan zaman lafiya da yadda Najeriya za ta iya zama madubin duba ga sauran kasashen duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Fadar shugaban kasa, Abuja - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Mufti Ismail ibn Musa Menk, ya ziyarci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba.
Da yake jawabi bayan taron, Mufti Menk wanda ya kasance shugaban sashin wa'azi na majalisar malaman Islama a kasar Zimbabwe, ya ce shi da sauran malaman Musulunci sun kasance a Abuja ne don halartan taron zaman lafiya da hadin kai da aka shirya a karshen makon nan.
Malamin wanda ya ce tawagar malamai a fadin duniya sun kasance a Lagas a makon jiya saboda wani taro makamancin wannan, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da aminci a tsakanin daukacin yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaman lafiya ke sa kasa ta samu nasara, Mufti Menk
A cewarsa, ta hanyar zaman lafiya da mutunta juna ba tare da la'akari da banbancin addini da salsala bane za a samu nasara a kasar, rahoton Channels Tv.
Ya ce manufar wannan taro ba wai don karfafa zaman lafiya a Najeriya bane kawai harma da sanar da muhimmancin zaman lafiya a tsakain al'ummarta.
Mufti ya kuma bayyana cewa kasashe kan gaza a yayin da al'ummominsu suka ki mutunta shugabanninsu.
Inda ya kara da cewar Najeriya na iya zama kasar da ta fi kowacce bunkasa a Afrika sannan ta zama madubin duba ga sauran nahiya idan al'ummanta suka yi maraba da shugabanninsu, suka bayar da gudunmawa mai kyau da yi wa kasar hidima cikin gaskiya da amana.
Jaridar Daily Trust ta nakalto Shehin malamin yana cewa:
"Dole mu zama mutane masu hadin kai, mu mutunta juna, shugabannin da muke da su, mu yaba masu, mu yarda da su. Ya kamata mu fahimci cewa idan har za mu mutunta shugabancinmu, za mu samu ci gaba a matsayinmu na kasa. Idan ka duba kasashen da suka gaza saboda rashin mutunta shugabancinsu ne kuma a zahiri sun gaza a sakamakon haka.
"Amma idan za mu ba shugabanninmu goyon baya sannan mu tabbatar da ganin cewa kowannemu ya ba kasar nan gudunmawa mai kyau, Najeriya za ta iya zama kasa mafi bunkasa a Afrka, kuma magana ta gaskiya, na yarda cewa yawan jama'a, albarkatu da komai da muke da su a Najeriya ni kaina kasancewana dan Afrika daga Zimbabwe, a kodayaushe muna duba ga Najeriya a matsayin daya daga cikin mafi girman tattalin arziki."
Mufti ya yi hoto da Taaooma
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta kawo a baya cewa yar wasan barkwanci a Najeriya, Maryam Apaokagi wacce aka fi sani da Taaooma, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa hotunanta tare da fitaccen malamin Musulunci Mufti Menk.
A kasan wallafar tata, Taaoma ta bayyana tattaunawar da ta yi da Mufti.
Asali: Legit.ng