Atiku, Obi vs Tinubu: CJN Ariwoola Ya Bayyana Wajen Daukaka Kara Bayan Kotun Koli
- Mai shari’a Olukayode Ariwoola, Alƙalin Alƙalan Najeriya (CJN), ya ce duk mai son ɗaukaka ƙara bayan kotun ƙoli, sai dai ya je kotun Allah
- CJN, a cikin wani faifan bidiyo, ya ce kotun ƙoli ita ce kotun ƙarshe da za a iya sauraron ƙara domin yin adalci
- Kalaman na Ariwoola na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyun adawa ke nuna rashin amincewarsu da korar wasu gwamnoni da kotun ɗaukaka ƙara ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Olukayode Ariwoola, Alkalin Alƙalan Najeriya (CJN) a cikin wani faifan bidiyo ya bayyana cewa duk wanda ke neman adalci a Najeriya ba zai iya wuce kotun ƙoli ba, inda ya ƙara da cewa ita ce kotun ƙarshe a Najeriya.
A cikin faifan bidiyon, CJN ya bayyana cewa duk wanda bai gamsu da hukuncin da kotun koli ta yanke ba a kowace shari'a, to ya kai kukansa wajen Allah, inda ya ƙara da cewa babu wata kotu bayan kotun ƙoli.
Wani mai amfani da sunan @omoelerinjare a Twitter ya sanya bidiyon a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, a daidai lokacin da wasu ke nuna adawa da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na korar wasu gwamnoni, musamman na ƴan adawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan ƙotun ƙoli sai kotun Allah, CJN Ariwoola
Kalaman na Ariwoola sune irin su na farko tun bayan da kotun ƙoli ta yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar da Peter Obi da ƴan takarar jam’iyyar PDP da na LP suka shigar a zaben shugaban ƙasa na 2023.
Atiku da Obi sun shigar da ƙara kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
CJN ya bayyana cewa:
A kotun da na ke jagoranta ne na samu damar zama ɗaya daga cikin ma'aikatan shari'a da suka danganci sauraron ƙararraki."
"Kamar yadda muka sani, kotun ƙoli a Najeriya, ita ce kotun ƙarshe, don haka duk hukuncin da aka yanke, ɗaukaka ƙara yana wajen da babu wanda daga cikinmu da muke zauna a nan ya taɓa zuwa, a gaban Allah."
An Caccaki CJN Ariwoola
A wani labarin kuma, alƙalin kotun ƙoli mai ritaya, mai shari'a Muhammad Dattijo, ya yi suka kan ƙarfin ikon da aka ba alƙalin alƙalan Najeriya, Kayode Ariwoola.
Mai shari'a Muhammad ya nuna damuwarsa kan yadda aka kafa kwamitin alƙalan sauraron ɗaukaka ƙarar zaɓen shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng