Bidiyo: Atiku Ya Ziyarci Makarantar da Ya Yi Karatu a Adamawa, Ya Bada Kyauta Ga Dalibai Masu Hazaka

Bidiyo: Atiku Ya Ziyarci Makarantar da Ya Yi Karatu a Adamawa, Ya Bada Kyauta Ga Dalibai Masu Hazaka

  • Atiku Abubakar ya ziyarci makarantar da ya yi karatu ta ' Central Primary School' a Jada, jihar Adamawa a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa bidiyon ziyarar tasa a soshiyal midiya, yana mai nuna jin dadi da cikar muradi
  • A yayin ziyarar, Atiku ya ba da gurbin karatu kyauta da kyaututtuka ga dalibai masu hazaka a masarautar Ganye da ke jihar Adamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Adamawa, Yola - Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar ya ziyarci makarantarsa ta firamare a Jada, jihar Adamawa a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wallafar da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) inda ya bi sa da hotuna da bidiyoyi.

Kara karanta wannan

Ku bar ganin Ganduje haka; raina kama ne kaga gayya - Jigo a PDP ya ankarar da Kwankwaso

Ya yi wa bidiyon take da:

"Cike da farin ciki. Yau na koma inda komai ya fara. Makarantata, Central Primary School, Jada. -AA"

Atiku ya kara da cewar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin farin ciki da cikar buri ne komawa makarantata, Central Primary School da ke Jada, inda na ba da tallafin karatu da kyaututtuka ga dalibai masu hazaka a masarautar Ganye ta Jihar Adamawa. -AA"

Yan Najeriya sun yi martani yayin da Atiku ya ziyarci makarantarsa ta firamare

Kamar koda yaushe, yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi na shafin Atiku don bayyana ra'ayoyinsu kan ci gaban.

@woye1 ya wallafa:

"Yallabai Atiku yana kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa a 2027 cikin dabara. Duk da haka zai fadi ne."

@alakowee ya rubuta:

"Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya wanda baya bisa ka'ida ba zai taba yin wannan ba!

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

"Bola Ahmed Tinubu ya ji kunya kan yaudarar yan Najeriya."

@omorogiec ya rubuta:

"Na san wani shugaban kasa wanda yan kasarsa basu san sunan makarantarsa na firamare da sakandare ba."

@IamThatNaijaGuy ya rubuta:

"Shin Tinubu zai iya ziyartar makarantarsa ta firamare kamar yadda Atiku ya yi? Ina so na duba wani abu ne."

NNPP ta yarda su hade da Atiku

A wani labarin, mun ji cewa jami'yyar NNPP ta amince da tayin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar na hadaka.

Wannan na zuwa ne bayan Atiku ya nemi 'yan jam'iyyun adawa da su zo a hada kai don kwato mulki daga APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng