Gudanar da Ayyukan Ofis Ya Sanya Gwamnan PDP Kashe N6bn Cikin Wata 3 Kacal
- Cikin wata uku kacal gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kashe N6bn wajen gudanar da ayyukan ofishinsa
- Gwamnan a ƙashin kansa ya kuma kashe Naira miliyan 209 a cikin wata uku a rahoton kasafin kuɗin jihar da aka fitar
- Rahoton ya nuna cewa alawus na jin daɗin jama'a, siyan abinci da kayan sha sun laƙume Naira biliyan 2 a cikin wata 3
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya kashe Naira biliyan 6 domin gudanar da ayyukan ofishinsa cikin watanni uku, kamar yadda rahoton kasafin kuɗin jihar ya nuna.
Rahoton kasafin kuɗi na kwata ta uku na shekarar 2023 na jihar Osun ya nuna cewa an kashe Naira miliyan 209 domin amfanin ƙashin gwamnan, cewar rahoton Daily Trust.
Rahoton, wanda aka sanya a shafin yanar gizo na gwamnatin jihar, ya tattara bayanan kuɗaɗen shiga da kuɗaɗen da aka kashe tsakanin watan Yuli da Satumba 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da rahoton ya yi cikakken bayani kan yadda gwamnatin jihar ta kashe kuɗaɗen, ta yi shiru kan kuɗaɗen shigar da jihar ta samu a cikin wa'adin da ake magana a kai.
Yadda gwamna Adeleke ya kashe N6bn
A cewar rahoton, ofishin Adeleke ya kashe zunzurutun kuɗi har naira biliyan 6 a cikin watanni uku kacal. Babu wani bayani kan takamaiman abubuwa ko ayyukan da aka kashe kuɗin a kansu, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.
Majalisar dokokin jihar ta kuma kashe sama da Naira miliyan 800 a cikin wannan lokacin.
Gwamnatin Osun ta kuma ce ta kashe sama da Naira Biliyan 2 wajen siyan abinci da kayan sha da alawus na jindaɗi ga jami'anta.
Bayan sauka mulki, Muhammadu Buhari ya faɗi manufa 1 tal da ta sa ya canza takardun naira a Najeriya
Bayani kan yadda aka kashe Naira bliyan 2 ɗin ya nuna cewa an kashe Naira biliyan 1.75 wajen jin daɗin jama'a yayin da N456,401,074.13 aka yi amfani da su wajen ababen sha da abinci.
Haka kuma a cikin rahoton, gwamnatin ta ce ta kashe Naira miliyan 400 wajen wayar da kan jama'a da tallace-tallace.
Adeleke Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Tsige CJ
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi amai ya lashe kan tsige alƙalin alƙalai (CJf na jihar.
Tun da farko gwamnan ya tsige mai shari'a Adepele Ojo tare da naɗa mai shari'a David Afolabi a matsayin muƙaddashin CJ. Sai dai, gwamnan ya sauya shawara kan wannan naɗin da ya yi.
Asali: Legit.ng