Hauhawan Farashin Kaya Zai Jefa Yan Najeriya Miliyan 2.8 Cikin Kangin Talauci, Bankin Duniya

Hauhawan Farashin Kaya Zai Jefa Yan Najeriya Miliyan 2.8 Cikin Kangin Talauci, Bankin Duniya

  • Babban Bankin Duniya (WB) ya yi hasashen cewa akalla 'yan Najeriya miliyan 2.8 ne za su shiga kangin talauci nan da karshen shekarar 2023 zuwa 2024
  • Bankin ya ce za a samu karuwar wadanda za su talauce ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kuma karancin habakar tattalin arzikin Najeriya
  • Sai dai rahoton bankin ya yi nuni da cewa ana sa ran zuwa cikin shekarar 2024, za a samu sassauchi kan hakan, ma damar gwamnati ta dauki matan da ya dace

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Washington, United States - Babban Bankin Duniya ya bayyana cewa, hauhawar farashin kayayyakin masarufi da karancin habakar tattalin arziki a Najeriya zai kara jefa mutane miliyan 2.8 cikin talauci nan da karshen shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Bayan sauka mulki, Muhammadu Buhari ya faɗi manufa 1 tal da ta sa ya canza takardun naira a Najeriya

Wannan bayanin ya biyo bayan wani rahoto mai taken, ‘Nazarin habakar talauci: Bincike da hasashe a kasashen da ke tasowa na duniya,’ wanda aka fitar kwanan nan.

Talauci zai karu a Najeriya a shekarar 2024
Ana sa ran yawan ‘yan Nijeriya da za su shiga ma'aunin talauci a duniya zai kai kololuwa a shekarar 2024 da kashi 38.8. Hoto: Lucy Ladidi Elukpo
Asali: UGC

Dalilin karuwa talauci a tsakanin 'yan Najeriya a 2023 - WB

Babban bankin, wanda ke a Washington ya ce,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“ya zuwa karshen shekarar 2023, hauhawar farashin kayayyaki da kuma karancin ci gaban tattalin arziki za su jefa mutane miliyan 2.8 cikin talauci."

Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 24.1 a watan Yulin 2023, kuma hakan ya faru ne sakamakon hauhawar farashin kayan abinci da kuma tasirin cire tallafin mai da aka yi a kasar.

Bankin na duniya ya kuma bayyana cewa an samu karuwar kashe kudi a kasar zuwa kashi 63 a 2023 fiye da a shekarar 2022, sakamakon karuwar kudaden ruwa, da karin kudaden da ake kashewa gabanin zabuka, da kuma kudin tallafin man fetur da ake biya.

Kara karanta wannan

Rahoto ya hango tsananin tashin farashin kayayyakin abinci a shekarar 2024, ga dalilin da ya ja

Tattalin arzikin Najeriya zai farfado a 2024 - WB

Bankin ya kara yin hasashen cewa ci gaban tattalin arzikin Najeriya nan gaba zai dogara ne kan ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da za su habaka hanyoyin samun kudaden shiga.

Hakanan ana sa ran hauhawar farashin kayayyaki zai fara daidaituwa nan da shekarar 2024, rahoton newsnownigeria.

Ana sa ran yawan ‘yan Nijeriya da za su shiga ma'aunin talauci a duniya zai kai kololuwa a shekarar 2024 da kashi 38.8 kafin a fara samun raguwar hakan sannu a hankali.

Jerin jihohin Najeriya da suke da masifar tsadar kayan abinci

Legit Hausa ta yi nazari kan jihohin Najeriya da suka fi tsadar kayan abinci, har zuwa wadanda ake sayar da kayan abincin da arha.

An samar da jaddawalin ne bisa kason da kowacce jiha take da shi na hauhawar farashin kayan abincin, kamar yadda shafin kididdiga na TheCableIndex ta wallafa a shafin ta na X.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.