'Mu bayinka ne?’ Sanatan LP Ya Yi Wa Akpabio Kaca-Kaca a Zauren Majalisar Dattijai

'Mu bayinka ne?’ Sanatan LP Ya Yi Wa Akpabio Kaca-Kaca a Zauren Majalisar Dattijai

  • Mamba mai wakilatar Anambra ta Arewa ya dakawa shugaban majalisar dattawa tsawa bayan da ya sanar da shugabannin bangaren marasa rinjaye na majalisar
  • Akpabio ya sanar da Abba Moro matsayin shugaban marasa rinjaye; da kuma Osita Ngwu matsayin bulalar marasa rinjaye
  • Sai dai wannan nadin bai yi wa Sanata Tony Nwoye dadi ba, inda ya tambayi shugaban majalisar "ko mu bayinka ne?", nadin da ya kira rashin adalci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An samu hayaniya a zauren majalisar dokokin tarayya a ranar Talata bayan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya sanar da sabbin nade-nade na shugabannin marasa rinjaye.

Akpabio ya nada Abba Moro sanata mai wakiltar Benue ta Kudu a matsayin shugaban marasa rinjaye; da kuma Osita Ngwu, sanata mai wakiltar Enugu ta Yamma a matsayin bulalar marasa rinjaye.

Kara karanta wannan

Yanzu: An samu sabon Kakakin Majalisa da Mataimakinsa a Filato

Majalisar Dattawan Najeriya
Sanata Tony Nwoye ya ce rashin adalci ne shugaban majalisar ya zabi shugabanni na bangaren marasa rinjaye. Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

'Yan jam'iyyar PDP sun maye gurbin Simon Mwadkwon, sanata mai wakiltar Filato ta Arewa; da Darlington Nwokocha, sanata mai wakiltar Abia ta tsakiya, The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Tony Nwoye na LP ya harzuka, ya yi wa Akpabio tsawa

Jim kadan bayan da Akpabio ya kammala yin sanarwar da aka ce ta fito ne daga kusoshin ‘yan majalisar na bangaren marasa rinjaye, sai hatsaniya ta kaure a zauren majalisar, Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Tony Nwoye na LP, sanata mai wakiltar Anambra ta Arewa, ya ce rashin adalci ne shugaban majalisar dattawa ya zabi shugabanni ga bangaren ‘yan majalisar marasa rinjaye.

“Mu bayinka ne? Me yasa shugaban majalisar dattawa zai zabo mana shugabanni?”

Nwoye ya yiwa shugaban tsawa.

“Ka yi mafi munin hakan, yanzu ka kai mu makura, me hakan ke nufi ne? Wannan ba adalci ba ne, ba wai ina magana a kaina ba ne, batu ne akan shugabancin majalisar dattawa."

Kara karanta wannan

Ba bayin ka ba ne mu, sanatoci sun yi wa Akpabio rashin kunya kan dalili 1 tak, ya yi bayani

“Kowane lokaci, kune ke ci gaba da zabar mana jagorori. Mu bayinka ne? Yadda aka zabe ka haka muma zabar mu aka ayi, babban abin da za ka iya yi shi ne dakatar da ni."

- cewar Nwoye

Akpabio ya yi martani

Bayan wasu Sanatoci sun tausasa Nwoye, Akpabio ya bayyana cewa ya yi sanarwar ne bayan da 'yan majalisar biyu suka gabatar da sa hannun 'yan majalisar dattawan da suka aminci da nadin su.

"Ni ina aiki da abinda ya zo gabana ne kawai" .

- cewar Akpabio

Tsohon minista ta zama sabon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa

Legit Hausa ta ruwaito maku cewa, tsohon ministan harkokin cikin gida kuma Sanata a karo na huɗu a inuwar PDP, Sanata Abba Moro, ya zama sabon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da naɗin a zauren majalisar dattawa da ke Abuja ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.