Bayan sauka mulki, Muhammadu Buhari Ya Faɗi Manufa 1 Tal da Ta Sa Ya Canza Takardun Naira a Najeriya

Bayan sauka mulki, Muhammadu Buhari Ya Faɗi Manufa 1 Tal da Ta Sa Ya Canza Takardun Naira a Najeriya

  • Muhammadu Buhari ya bayyana muhimmin dalilin da ya sa gwamnatinsa ta canza fasalin Naira ana dab da zaɓen 2023
  • Tsohon shugaban kasan ya ce ya yi haka ne domin nuna wa yan Najeriya cewa babu hanyar samun mulki cikin sauƙi
  • Ya kuma ce gwamnatinsa ta samu nasara gagara misali a ɓangarorin tsaro da kuma tattalin arzikin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi bayanin manufar sake fasalin Naira da gwamnatinsa ta bullo da shi a lokacin da ake tunkarar babban zaɓen 2023.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Buhari: Na Canza Takardun Naira Ne Saboda Toshe Hanyar Samun Mulki da Sauki Hoto: Muhammadu Buhari, CBN
Asali: Twitter

Buhari ya bayyana cewa ya canja fasalin Naira ne domin nuna wa ƴan Najeriya babu hanyar samun mulki cikin sauƙi, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya roƙi 'yan Najeriya muhimmin abu 1 da zai taimaka wajen yaƙar ta'addanci a arewa

Tsarin sauya kuɗin da babban bankin Najeriya (CBN) ya aiwatar a karkashin gwamnan lokacin, Godwin Emefiele, 'yan Najeriya da dama na ganin ya haifar da kunci saboda karancin takardun kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hirar da ya yi ta farko tun bayan barin mulki, wadda aka watsa a daren ranar Litinin a gidan talabijin na Najeriya (NTA), Buhari ya ce:

"Abin da ya sa muka yi haka shi ne domin ƴan Najeriya su gane kuma su amince cewa babu wata hanya mafi sauki wajen hawa kan gadon mulki saboda mulki ba abu ne mai sauƙi ba."
"Kamar yadda na sha nanatawa na nemi takara sau uku amma duk sai dai na kare a kotun kolin Najeriya."
‘Yan Najeriya da dama za su ce wannan wauta ce. Sun gwammace su sami hanya mafi sauƙi da sauri wajen hawa mulki, kuma hanyar ita ce su tara kuɗi ta yadda zasu yaudari mutane su cimma burinsu."

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta tabbatar da sabon muhimmin naɗin da Shugaba Bola Tinubu ya yi

Muhimman wuri biyu da na samu nasara - Buhari

Buhari ya ce manyan nasarorin da ya samu ita ce ta fannin tsaro da tattalin arziki, yana mai cewa a karkashin gwamnatinsa an kwato yankunan da Boko Haram ta kwace a jihar Borno.

Tsohon shugaban kasar, wanda ya ce bai taba daukar sha'anin ‘yan Najeriya da wasa ba, ya ce bai tara kadarorin haram ba tsawon shekaru takwas a kan mulki.

Gwamna Lawal ya nuna alamjn doke Matawalle

A wani rahoton kuma Dauda Lawal ya ce yana da kwarin guiwar shi zai doke ƴan adawa a zaben da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi umarnin a sake a Zamfara.

Gwamnan na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa APC na hassada ne da ɗumbin ayyukan ci gaban da ya zuba a jihar cikin watanni 5 kaɗai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel