“Yadda Na Koma Kwana a Karkashin Gadar Oshodi Bayan Shafe Shekaru 21 a Amurka,” Wani Mutum Ya Koka

“Yadda Na Koma Kwana a Karkashin Gadar Oshodi Bayan Shafe Shekaru 21 a Amurka,” Wani Mutum Ya Koka

  • Cikin hawaye, wani mutum ya ba da labarin yadda ya dawo cikin hankalinsa a karkashin gadar Oshodi da ke Lagas bayan shafe fiye da shekaru 20 a Amurka
  • A cewarsa, wani banki ya dauki nauyin tura shi turai karatu wato birnin Landan inda ya shafe tsawon shekaru tara yana karatu a bangaren hada-hadar kudi
  • Ya tuna yadda ya yi mafarki mai ban mamaki inda yake tashi sama sannan aka yi masa maraba da zuwa Bahamas sannan kuma ya tafi Landan daga karshe ya isa Najeriya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani matashi dan Najeriya ya magantu kan yadda ya tsinci kansa yana kwana a karkashin gadar Oshodi, Lagas bayan ya shafe tsawon shekaru 21 a Amurka.

Kara karanta wannan

“Da na koma Jamhuriyar Nijar”: Buhari ya magantu kan zaryar da wasu ke yi a gidansa na Daura

A wata hira da aka yi da shi a gidan radiyo wanda @instablog9ja ta watsa, mutumin ya ba da labarinsa mai ban al'ajabi cikin hawaye.

Wani dan Najeriya ya koka bayan shafe shekaru 21 a Turai
“Yadda Na Koma Kwana a Karkashin Gadar Oshodi Bayan Shafe Shekaru 21 a Amurka,” Wani Mutum Ya Koka Hoto: @instablog9ja
Asali: Twitter

Ya yi mafarki mai ban mamaki

Da yake magana a harshen Yarbanci, mutumin ya ce wani banki ne ya dauki nauyin karatunsa zuwa Landan inda ya karanci bangaren hada-hadar kudi na tsawon shekaru tara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwa sun dauki sabon salo a rayuwarsa bayan ya yi wani mafarki mai ban mamaki a wata rana. A cikin mafarkinsa, yana ta tashi a sama sannan ya tsinci kansa ana yi masa maraba da zuwa Bahamas inda ya kan je hutu.

Abu na gaba, aka yi masa maraba da zuwa Landan, zuwa Afrika sannan sai Najeriya. Ya sake shiga rudani a mafarkin lokacin da ya fara jin hayaniyar motocin da ake kira 'molue' a Lagas.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda budurwa ta shararawa saurayi mari bayan ya nemi ta aure shi ya girgiza intanet

Ya ce yayyunsa maza ne suka jefa shi halin da yake ciki

Bayan mafarkin, ya ce an gaggauta kwasansa zuwa wani asibiti a California kasancewar ya kamu da rashin lafiya. Sai ya lura cewa baya gane kansa tun daga lokacin.

Kan yadda ya san cewa yana kwana a karkashin gada a Oshodi, Lagas, mutumin ya ce yan sanda ne suka kama shi, kuma a lokacin ne duhun kansa ya yaye.

Ya zargi yan’uwansa da alhakin jefa shi a halin da suke ciki.

A cewarsa, sun tarbe shi a filin jirgin sama, suka kwashe kayansa sannan suka yasar da shi a asibitin masu tabin hankali da ke Yaba kuma bayan wata shida babu wani dan uwa da ya zo nemansa, aka jefar da shi waje, a haka ya kai ga Oshodi.

Kalli bidiyn a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Mikkyyyyy_ ya ce:

"Wannan abun bakin ciki ne gaskiya, wannan Najeriya wata aba ce ta daban fa, kada Allah ya sa Najeriya ya faru da mu."

Kara karanta wannan

“Na zata ba zai yiwu ba”: Tsoho dan shekaru 87 ya fada tarkon son kawar diyarsa, ya yi wuff da ita

@Realtonyblack1:

"Ya Allah kariyarka shine abun da nake nema, kuma kada ka barni na yi wadanda ba za su yafe mun ba laifi....muguguntan yan uwa ya fi komai girma!!!!" '

@IamBlaccode:

"Ga wadanda ke cewa babu asiri...Ga misali nan. Wannan abu akwai karya zuciya! Ya kamata yan uwansa su ji kunyar kansu. Ina fatan abubuwa za su daidaita a rayuwarsa."

Budurwa ta shararawa manemin aurenta mari

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani bidiyon neman aure da aka samu tangarda ya bayyana a soshiyal midiya kuma ya haddasa cece-kuce a tsakanin al'umma.

Wani mai suna @cliifforrd, ya yada bidiyon yayin da yake al'ajabin abun da mutane za su aikata da sune abun da ya faru da matashin ya ritsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng